Wace illa manhajar GB WhatsApp ke da shi? Wannan ita ce tambayar da aka fi yi min tun daga fitowar wannan fili na Kimiyya da Fasahar Sadarwa. Mutane da dama suna amfani da shi, amma ana ce musu yana da illa, to menene illar GB WhatsApp din?
Kafin mu shiga gundarin magana a kan illar GB WhatsApp din, sai na dan yi tsokaci a kan matsalar da aka samu shekarar da ta gabata, na katsewar manhajar Facebook, WhatsApp da Instagram na tsawon awanni 6, wanda hakan ya jawo wa mamallakinsu asarar Daloli masu yawa.
Kamar yadda suka saba, wasu gungun madatsa ‘hackers’ suka samu nasarar yin kutse a manhajojin Facebook, WhatsApp da Instagram wanda hakan ya sa suka daina aiki na tsawon awanni 6. To abin tambayar shi ne, ta yaya hakan ya faru? Madatsan sun yi wa kamfanin ba za ta ne, ta yadda suka kutsa, wanda hakan ala tilas ya sa kamfanin ya sauke Serber dinsa, dalilin da ya sa kenan suka daina aiki a lokaci guda tsawon awanni 6, kasancewar duka kamfanin daya ne ba matsalace ta na’ura ko wani abu ba, mummunan hari ne daga hackers, kuma wannan shi ne hari mafi muni da kamfanin ya taba fuskanta tun bayan kafuwarsa. Sau biyu kenan kamfanin na fuskantar hari irin wannan a shekarar 2021.
Daga lokacin da Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aikin na tsawon awa 6, kamfanin ya tafka mummunar asara ta kudi kimanin Dalar Amurka Bilyan 7, wanda ya yi daidai da Naira Tiriliyon 3, kamar yadda jaridar Bloomberg ta ruwaito.
Wasu suna alakanta faruwar hakan da irin nuna wariya kamfanin Facebook din suke yi, haka kawai sai su rufe wa wanda suke ki account dinsu na facebook da kuma shiga sabgar siyasar Diplomasiyya na wasu shugabannin duniya da katsalandan kan wasu al’amuran da basu shafe su ba.
Wannan abin da ya faru da facebook zai zama izna ga mutanen da suka mayar da facebook hanyar neman kudi ta kowace irin hanya mai kyau da marar kyau. An tsayar da shi na tsawon awa 6 kacal, mutane sun gigice, sun shiga tashin hankali kamar ba za a iya rayuwa ba idan babu su. To kuwa ba a san me zai faru a gaba ba, wannan kamar dan ba ne, don tabbas hackers din nan ba hakura za su yi ba. Don ma yanzu shi Mark Zuckerbag din yana ta bin hanyoyin da suka dace don ganin hakan bai sake faruwa ba.
Menene Illar GB WhatsApp?
Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana wasu tsarurruka da ‘Whatsapp’ na asali ba shi da su, kamar irinsu adana (sabing) na hoto, bidiyo, ko kuma kwafin rubutu daga ‘status(es)’ na mutane kai tsaye, ko boye alamar karantawa ko karbar sako, ko don yana nuna alamar in mutum yana online, ko don tura ‘file’ mai nauyi, ko boye groups/chats, ko rubuta sunan ‘group’ da harafai sama da 35, yin status da harufai 250, a takaice, GBWhatsapp yana da wasu ‘features’ da normal whatsapp.com ba shi da su.
Amma, yana da kyau mutum ya sani cewa duk wadannan tarko ne na masu kutse ko madatsa ‘hackers’. Sun tsara shi ne ta yadda zai baka sha’awa sosai, fiye da manhajar WhatsApp ta asali (normal Whatsapp), tare da baka damar wasan buya da ma’abota amfani da normal Whatsapp, musamma ma mata. Ka tura sako, a karanta, amma ba za ka ga alamar an karanta ba, sannan a duba status dinka ba tare da ka ga wanda ya gani ba.
To dai maganar gaskiya, kai tsaye, GBWhatsapp, ‘mod’ ne, ma’ana ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an kirkire shi da ‘code’ (tsari) irin an Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba. Ina shawartar masu amfani da GBWhatsapp, da masu sha’awar amfani da shi, da su kauracewa manhajar saboda wadannan dalilai; shi GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp, ‘AledMods’ ne suka yi shi, ba su da lasisi, kuma sun karya ka’idar kirkirar da bada lamunin amfani da sirrikan jama’a. Shi ya sa ba za ka sami manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba. Kai! Ka ma taba ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa babu, saboda ba su da gaskiya.
Mai amfani da GBWhatsapp, ya sani cewa duk wasu bayanai da suke cikin wayarsa, wannan manhaja na iya tattarewa, babu wani sirrin cikin wayarka da ba za su iya lekawa ba, siyarwa, ko amfani da shi a duk lokacin da suka dama.
Idan aka turo ma wani sako mai dauke da ‘birus’ GBWhatsapp ba shi da wasu matakan kare ka daga cutarwarsu. Kai! Shi ma kansa ‘spyware’ ne. Duk abin da kake a GBWhatsapp, tsirara kake, shi ya sa, yawancin wadanda ake musu kutse (hacking) na Whatsapp, masu amfani da Whatsapp Mods ne, irin su GBWhatsapp, WhatsappPlus, Whatsapp Gold, Clones, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YOWhatsapp da sauransu.
GBWhatsapp ba ya restore (dawo da bayanai) a wasu lokutan, kamar yadda na fada a sama, asali manhajar ta saba wa tsarin Google, kuma ana backup ne (yawanci) da Google account. Shi ya sa, da zarar ya yi ‘edpire’ (wani lokaci) za ka rasa duk bayananka, har ‘groups’ da kake ciki, sai ka nemi a maida ka. Ka lura, a duk lokacin da ka dauko shi daga yanar gizo, in dai wayarka tana ‘security patching’ (kula da tsaro), za ta gargadeka cewa, wannan app din zai iya cutar da kai, ko bayananka, ba ka taba lura ba ko? In ka taba lura da haka, don me za ka yarda?
Kai tsaye GBWhatsapp na mayaudara ne, in ba su cuceka yau ba, za su iya cutar da kai gobe. Kuma a kowane lokaci, Whatsapp na asali, za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da dandalin na har abada.