Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuma dan kasar Faransa, Karim Benzema, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar duniya (Ballon D’Or).
Kyautar wanda manyan ‘yan jaridun duniya ke kada kuri’a wajen zaben dan wasan da ya fi nuna hazaka a kwallon kafar duniya, sun zabi Benzema a matsayin gwarzo a karo na 66.
- Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Ci Gaba Da Farfadowa A Bana
- Ya Kamata Jama’ar Kasar Sin Su Yi Kokari Tare Don Sa Kaimi Ga Farfadowar Al’ummar Kasar Sin
Kyautar wadda ake gudanar da ita duk shekara a kasar Faransa, ta samu halartar manyan tsofaffin ‘yan wasan duniya irin su Ronaldo, Figo, Drogba da sauransu.
Benzema ya zo a matsayin na daya, inda ya doke dan wasan Manchester City Debrune da Sadio Mane na Bayern Munich da kuma Robert Lewandoski na Barcelona.
Tuni dai manyan ‘yan wasa da abokan Benzema suka shiga taya shi murnar lashe wannan kyauta.
Benzema ya samu nasarar lashe kyautar ne bayan bajinta da ya yi a 2022 a gasar Laliga da kuma gasar zakarun turai.
Tsohon dan wasan gaban Barcelona, Lionel Messi ne ya lashe kyautar a shekarar 2021.