Kotu a birnin Maradi da ke Jamhuriyar Nijar ta yanke wa wasu matasa hukuncin ɗaurin shekara uku-uku a gidan yari, bayan samunsu da laifin naɗa da kuma yaɗa wani bidiyo da ke nuna wasu mata biyu suna madigo.
BBC ta rawaito cewa, wadanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da mata 13 da namiji ɗaya.
- ‘Ƴar Majalisa Na Burin A Samar Da Tsauraran Dokoki Kan ‘Yan Luwadi Da Madigo A Nijar
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane Fiye Da 130 Cikin Wata Biyu A Nijar
Baya ga hukuncin ɗaurin, kotun ta ci tarar matan su 13 Sefa miliyan ɗaya kowace yayin da aka ci namijin tarar sefa miliyan uku kasancewarsa wanda ke da dandalin manhajar Whatsapp din da aka yadda wannan bidiyon.
Makonni biyu da suka wuce ne dai aka fara gurfanar da mutanen 14 gaban kotun bisa zarginsu da aikata laifin yaɗa abu ta shafukan intanet da ka iya tayar da hankalin jama’a.
Laifin, a cewar lauya mai shigar da ƙara ya saɓawa dokar haramta aikata laifuka ta shafukan intanet.
Ya kuma nemi a yi mu su hukunci mafi tsanani na ɗaurin shekaru uku; wanda kuma shi ne kotun ta sanar a ranar Alhamis.
Jami’an tsaro na jandarma ne suka kakkama matasa bayan wani koke da wasu mutane suka yi kan yaɗa bidiyon na batsa.
Dukansu dai an same su da laifin yaɗa abubuwan batsa da nuna tsiraicin ɗan adama da kuma tayar wa jama’a hankali.
Sai dai kotun ta ba su damar ɗaukaka ƙara a cikin kwana 10, kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada.
Wannan shari’ar dai ta ja hankalin mutane a ciki da wajen ƙasar ta Nijar saboda yadda aka ce a farkon shari’ar aka yi ta muhawara kan wace doka za a yi amfani da ita wajen yi musu shari’a.
Hakan ya faru ne kasancewar dokokin ba su tanadi hukunci ƙarara da za a iya yankewa wadanda aka samu da aikata laifin luwaɗi ko maɗigo ba.
Ba mamaki wannan ne ya sa aka yi amfani da dokar haramta yaɗa abubuwa masu tayar da hankali a shafukan inta wajen yi musu shari’a.
Sakamakon haka dai yanzu haka wata ƴar majalisar dokokin ƙasar ta gabatar da ƙuduri gaban majalisar da ke neman yin dokar haramta luwadi da maɗigo a ƙasar mai rinjayen Musulmi da ke yammacin Afrika.