Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da samar da ayyukan raya kasa da samar da romon dimokuradiyya a birane da karkara da nufin yaki da fatara, wahalha da zaman kashe wando don ciyar da al’umma baki daya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a fadar shugaban kasa a birnin tarayya, yayin amsar lambar yabo daga cibiyar TBS da hadin guiwa da ofishin sakataren gwamnatin tarayya kan ayyukan sa na raya kasa da gina yankunan karkara.
- Shugaban Karamar Hukuma Ya Rufe Otal Kan Aikata Ayyukan Badala A Kebbi
- Zan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Kamar Yadda Buhari Ya Yi – TinubuÂ
Hadimin Gwamnan kan sabbin kafafen sadarwa, Lawal Mu’azu ya nakalto gwamnan na cewa lambar yabon za ta kara masa kumaji da haxaka wajen zage damtse domin hidimta wa jama’a.
Da ya ke sadaukar da lambar yabon da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika masa ga É—aukacin al’ummar jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya ce za ta kara masa karfin guiwa wajen cigaba da ayyukan jin kai kana yayi kira ga al’umma da su cigaba da marawa
gwamnatinsa baya don kai ga nasara musamman a sashen kiwon lafiya, hanyoyi da ingantaccen ilimi.
Gwamnan ya samu rakiyar uwargidan sa Aisha Bala Muhammad, shugaban jam’iyyar PDP reshen jiha, Ƙoshe Hamza Akuyam da Honorabul Auwal Jatau.
Saura sun hada da kakakin majalisar dokoki ta jiha Abubakar Suleiman da tsohon mataimakin gwamna Audu Sule Katagum.
Tun da farko Kakakin gwamnan Mukhtar Mohammed Gidado, ta cikin wata sanarwar da ya fitar, ya ce wannan lambar yabon kari ne kan wasu da dama da gwamnan ya samu bisa jajircewarsa wajen tabbatar da kai jihar Bauchi zuwa mataki na gaba.
Sanarwar ta ce, yadda gwamnan ya hummatu wajen shimfida ayyukan raya jihar ta birane da karkara, kiwon lafiya, gona, tsaro, samar da ayyukan dogaro da kai, da sauransu suna daga cikin fannonin da masu bada lambar yabon suka duba wajen karrama gwamnan.
LEADERSHIP Hausa dai ta labarto cewa gwamna Bala Muhammad na daga cikin mutum 44 da suka amshi lambar yabon daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Juma’a.