Tsohon Gwamnan jihar Yobe, kuma Sanata mai wakiltar shiyya ta daya (Zone A) a zauren majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ibrahim Gaidam tare da hadin gwiwa da Hukumar bunkasa yankunan kan iyakoki ta kasa: Border Communities Development Agency (BCDA)- sun kaddamar da tallafin kayan kiwon Kifi da sana’o’in dogaro da Kai ga matasa da mata sama da 400.
Da ya ke kaddamar da raba tallafin babban dakin taron karamar hukumar Damaturu, a babban birnin jihar Yobe, ranar Asabar, Sanata Gaidam wanda Muhammad Kiwata ya wakilta ya ce wannan kokari domin tallafa wa al’ummar mazaba da kayan sana’o’i hadi da horar da mata da Matasa, suna daga cikin abubuwan da Sanata Gaidam ke yi don kawar da zaman kashe wando domin samar da sana’a don jama’a su dogara da kansu.
Gaidam ya ce ya zama wajibi a matsayin su na shugabannin al’umma su tashi tsaye wajen samarwa da mata da matasa ayyukan yi musamman sana’o’in dogaro da kai, bayar da horo tare da tallafa musu da abubuwan da za su fara sana’o’in a lokacin da suka kammala samun horon.
Ya ce, “Saboda haka ne, ta hanyar hadin gwiwar fadar shugaban kasa mu ka yi kokarin bayar da tallafin wadannan kayan fara sana’o’i ga matasanmu sama da 400; domin kiwon Kifi wanda hakan zai taimaka su tsaya da kafafunsu.”
A nashi bangaren, babban jami’in Hukumar BCDA, Mista Rotimi Taiwo ya bukaci matasan su yi amfani da kayan da aka raba musu ta hanyar da ta dace, tare da sanar dasu cewa jami’an hukumar zasu biyo sawu domin tabbatar da cewa matasan basu sayar da kayan ba. Ya yi barazanar mika duk wanda aka kama da sauya akalar kayan zuwa hukumar EEFC.
Wakilinmu ya zanta da wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, daga karamar hukumar Yunusari, Fusama Alhaji Bai inda ya bayyana cewa, sun yaba matuka dangane da wannan tallafin da suka samu na gwamnatin Tarayya ta hanyar Sanata Gaidam.
Ya ce, “A matsayinmu na al’ummar mazabar Zone A suna alfahari da irin yadda Sanata Gaidam yake kokari wajen jawo hankalin gwamnatin tarayya domin inganta rayuwar yankunan da ke kan iyakar Nijeriya da makobciyarta Nijar. Wanda ko shakka babu hakan zai taimaka wajen farfado da yankunan.” In ji shi.