ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ambaliyar Ruwa: Jihohi 21 Sun Samu Kayayyakin Agaji –Sadiya Farouq

by Sulaiman
3 years ago
Sadiya Farouq

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa ma’aikatar ta rarraba kayan agaji ga dukkan jihohi 21 da bala’in ambaliyar ruwa ta shafa a sassa daban-daban na ƙasar nan a bana.

Ministar ta bayyana hakan ne a wajen taron da ta yi da manema labarai a ranar Talata a ofishin ta a Abuja domin bayyana irin ayyukan jinƙai da ma’aikatar, tare da haɗin gwiwa da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA), su ka kai a wuraren da ambaliyar ta shafa.

  • Karramawar Shugaban Kasa Ta Kara Min Ƙaimi – Sadiya Farouq

Ministar ta ce, “Zuwa yanzu jihohi 21 sun karɓi nasu kayan agajin, waɗanda su ka haɗa da Abiya, Adamawa, Anambara, Bayalsa, Ekiti, Inugu, Imo, Jigawa,
Kaduna, Kano, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Oyo, Sakkwato, Taraba, Yobe da Gundumar Birnin Tarayya.”

ADVERTISEMENT

Hajiya Sadiya ta ce sakamakon bala’in ambaliyar, kimanin mutum 1,427,370 su ka rasa matsugunan su, wasu 612 kuma su ka rasa rayukan su, sannan wasu 2,776 su ka samu raunuka.

Sadiya Farouq

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Ta ƙara da cewa yanzu haka akwai ƙwararru da ke gudanar da irin waɗannan ayyuka, musamman ganin cewa har yanzu akwai wasu Ƙananan Hukumomi da ba sa shiguwa saboda matsalar ambaliyar.

Ta ce: “Domin samun nasarar wannan aiki, mun haɗa hannu da sashen kai agaji na sojojin ƙasar nan, tare da sauran ƙwararru da ingantattun kayan aiki, domin amfani da su wajen isa ga wurare masu wuyar zuwa da kuma jama’ar da ke cikin haɗari.”

Ministar ta ba da tabbacin cewa har yanzu ana ci gaba da wannan aiki na kai kayan agaji ga jihohin da wannan ambaliya ta shafa.

Yayin da ta ke ƙarin haske game da kayan da ma’aikatar ta raba, ministar ta ce, “Abubuwan da mu ka raba, kaya ne na buƙatar gaggawa na abinci, waɗanda su ka haɗa da shinkafa, masara, garin rogo, man gyaɗa, wake da kayan dafa abinci.

“Kayan da ba na abinci ba kuma da aka kai domin samun matsuguni na wucin-gadi ga jama’ar da su ka rasa wurin zama sun haɗa da kwanon rufi, siminti, kusoshi, sili, barguna, tabarmin roba da kwano.”

Haka kuma ministar ta ce ma’aikatan ceto su na nan su na aiki wurjanjan tun da aka fara ambaliyar, su na kwashe wadanda bala’in ya shafa tare da sama masu matsuguni, kuma ana kai wasu asibiti domin su samu kula ba tare da bata lokaci ba.

Sadiya Farouq

Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a lamarin da su shigo cikin ƙoƙarin da ake yi na taimaka wa wadanda abin ya shafa. Ta ce, “Fatan mu shi ne sauran ma’aikatun gwamnati irin su Ma’aikatar Albarkatun Kiwon Lafiya, Ayyuka da Gidaje, Aikin Gona, da Yanayi za su zo mu hada gwiwa a taron manema labarai na gaba domin su ma su gabatar da nasu bayanan kan ayyuka su domin mu yi bayani kan wannan aikin agaji da mu ke yi.

“Ina yin kira kuma ga gwamnatoci a kowane mataki, musamman na jihohi da ƙananan hukumomi, da su ba ‘yan sanda da mu bayanan da su ka dace, sannan su taka rawa wajen aikin ceto, kamar yadda Tsarin Gaggawa kan Shirya wa Ambaliya da Ceto na Kasa ya tanadar, wato ‘Flood Emergency Preparedness and Response Plan’.

“Ina jinjina wa jama’ar garuruwa saboda dagewar su. Mun samu rahoton cewa a cikin ƙananan hukumomi 144, jama’a a garuruwa sun yi aiki tare wajen samar da agajin farko ga iyalan su da maƙwatan su.

“Tawagar masu aikin bincikowa da ceto jama’a, waɗanda aikin ɗauko jama’a da ba su agajin farko don ceton rayuwar su tare da ba su magani da takardar zuwa asibiti ya rataya a wuyan su, ya zuwa yanzu sun isa yankunan ƙananan hukumomi 199 a jihohi 25.

“Ana ci gaba da aiwatar da waɗannan ayyuka kuma ina kira ga jama’ar garuruwan da ke cikin haɗarin aukuwar bala’i da su tabbatar da sun bi gargaɗi da umarnin da waɗannan ma’aikatan su ke ba su domin su na aiki ne saboda su kare tare da ceto rayuka.

Sadiya Farouq

Ministar ta mika Godiya ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari saboda “goyon bayan da ya ba mu tare da ɗaukar mataki da sauri wajen magance matsalolin ambaliya.”

Ta ƙara da cewa: “Wata babbar tawaga za ta ziyarci wasu daga jihohin a makon gobe domin ɗorawa kan ayyukan ceto da agaji tare da gano sababbin matsaloli da kurakurai a ayyukan waɗanda ke bukatar a gyara su. Hakan zai ba gwamnati damar nazartar al’amarin a kurkusa tare da haɗuwa da waɗanda abin ya shafa da iyalan su.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Ta’addanci Ya Zama Tarihi, Nijeriya Na Cikin Aminci – Lai Muhammad

Ta'addanci Ya Zama Tarihi, Nijeriya Na Cikin Aminci - Lai Muhammad

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.