Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya shigar da karar gwamnatin tarayya a gaban kotu kan ci gaba da tsare shi da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ke yi.
A karar da aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, Kanu na neman a gaggauta sakin sa daga hukumar DSS tare da biyansa diyyar Naira biliyan 100 saboda tauye hakkinsa na ‘yanci da mutuncin dan Adam.
- Ana Zargin Wani Mahaifi Da Karya Hannun Jaririnsa Saboda Yana Damunsa Da Kuka
- Rashin Tsaro: Amurka Ta Umarci Jami’anta Su Fice Daga Abuja
Kanu ya ce karar ta zama dole ne biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya na yin biyayya ga hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 13 ga Oktoba, wanda ya yi watsi da tuhumar ta’addancin da ake yi masa.
Kotun, wadda Mista Mike Ozekhome, SAN, ya shigar a madadin Kanu, mai kwanan wata 21 ga Oktoba na dauke da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1945/2022.
Kanu ya ce an yi shari’ar ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin 1999.
“Saboda sashe na 46 (1) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da doka ta 1 da ta 2(1) na Dokokin Hakki (Tabbatar da Hukunci), duk mutumin da aka yi zargin cewa wani daga cikin tanade-tanaden na 4 na kundin tsarin mulkin kasar da ya ke, wanda yake da hakkin, ko ya kasance, ko kuma ana iya cin karo da shi a kowace jiha dangane da shi, na iya neman babbar kotun jihar domin ta yi masa hukunci.”
A cikin karar, Kanu yana son a bayyana cewa ci gaba da tsare shi da gwamnati ke yi daga ranar 13 ga Oktoba zuwa yau, ba daidai ba ne, zalunci, rashin sanin ya kamata ne, kuma ba bisa ka’ida ba.
“Ya keta hakkina na mutunta bil Adama, ‘yancin kai kamar yadda sashe na 34, 35, 36, 39, da 41 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tabbatar.
Kanu kuma ya nemi a umarci wadanda ake kara da su sake shi daga hannunsu ba tare da wani sharadi ba.
Ya sake neman a hana wadanda ake kara shiga hakkinsa ko mu’amala da shi ta hanyar da ta dace da hakkinsa na asali da kundin tsarin mulki na 1999 ya ba shi.
Bugu da kari, yana neman a biya shi diyyar Naira biliyan 100 ga wadanda ake kara saboda tauye masa hakkinsa.