Akalla ‘yan Nijeriya miliyan 93.5 ne aka yi wa rijista don kada kuri’a a zaben 2023, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana.
Da yake bayyana adadin wadanda aka tantance su kada kuri’a a zabe mai zuwa, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya miliyan 12.29 ne suka samu nasarar kammala sabuwar rajistar mallakar katin zabe a cigaba da rajistar masu kada kuri’a (CVR) da aka kammala.
Da yake magana a ranar Laraba a Abuja, yayin taron hukumar INEC zango na uku da ta ke gayyato duk jam’iyyun siyasa, Yakubu ya ce bayan tantance bayanan da aka yi ta hanyar amfani da manhajar tantance yatsun masu kada kuri’a (ABIS), an gano mutum sama da miliyan 2.78 da ke da gurbatacciyar rajistar kada kuri’a kuma nan take aka cire su daga rumbun ajiye bayanan hukumar.
Saboda haka, ya ce hukumar ta gano jami’anta 23 daga cikin masu yin rajistar masu kada kuri’a ta hanyar da bata dace ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp