Rundunar ‘yansanda a Jihar Sakkwato sun cafke wani mutum da ke da katin zabe sama da 100, watanni hudu kafin fara zaben 2023.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Muhammed Ussaini Gumel ne, ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Sokoto.
- Kisan Kai: Kwamishinan ‘Yansanda Ya Bada Umarnin Yin Bincike Kan Mutuwar Jami’in Dansanda A Kebbi
- Ya Kamata Amurka Ta Soke Takunkumi Idan Tana Son Taimakawa Afirka
Duk da cewa har yanzu hukumar ‘yansanda ba ta gano ainihin wadanda suka mallaki na’urar katin zaben ba, Gumel ya ce ana kyautata zaton masu wannan katin ba mazauna Sabon Birnin ba ne kadai inda aka kama wanda ake zargin.
Ya kuma yi kira ga jama’a musamman wadanda katinan zabensu ya bata, da su ziyarci hedikwatar hukumar inda za a duba katunan domin masu su su karbi abun su.
A cewarsa, an gurfanar da wanda ake zargin ta hanyar hujjoji da shaidun masu mallakar da suka fito a hedikwatar ‘yansanda don neman katinansu.
Jim kadan bayan kammala taron, kwamishinan ya kuma yi wa wasu sabbin jami’ai shida da aka kara wa karin girma ado da sabbin mukamai.
A halin da ake ciki, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta buga katin zabe na ‘yan Nijeriya cikin masu rajistar masu kada kuri’a daga ranar 15 ga watan Janairu zuwa 31 ga Yuli, 2022.
Kwamishinan INEC na kasa, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a cikin shirin Siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
Okoye ya ce, “Idan kai mai rijista ne, wato idan kana cikin ‘yan Nijeriya miliyan 84 da suka rigaya suka yi rajista, za ka iya bin diddigin bayananka a cikin rumbun adana bayananmu.
“Na biyu, idan kana daya daga cikin wadanda suka yi rajista da hukumar a ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a tsakanin ranar 28 ga watan Yunin 2021 zuwa ranar 14 ga watan Janairun 2022, za ka iya bin diddigin inda katin zabenka yake, ka karbe shi.”