Babban Limamin Masallacin Juma’a na Alfurkan da ke Unguwar Nassarawa GRA a Kano, Dakta Bashir Aliyu Umar ya yi kira da a guji yada kalamun kiyayya mai haddasa gaba a tsakanin al’umma.
Malamin yana daya daga cikin futattun mutane ‘yan asalin Kano da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karrama da lambar girmamaw ata kasa (O.O.N), ya bayyana cewa wannan lokaci da ake kusantar kakar zaban shugaban kasa da na ‘yan majalisa da gwamnoni akwai bukatar al’ummar Nijeriya su yi taka-tsan-tsan da iya bakina gujiwa yada kalaman kiyayya da ke haddasa gaba da kiyayya a tsakanin al`umma, ko da kuwa akwai bambamcin ra’ayi na siyasa ko na kabilanci ko sabanin addini, domin irin wadannan kalamai suna da mummunan hatsari wajan haddasa tashin hankali da ya keyakea kasa.
- Mutane 30 Sun Mutu Cikin Mako Daya A Hatsarin Mota A Kwara
- Jam’iyyar PDP A Kebbi Ta Shirya Tarbar Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar
A cewarsa, kamar yadda kalaman yada kiyayya ta haddasa mummunan bala’i na salwantar da dubun-dubatar mutane a kasar Rwanda, kamar yadda na jena gani da idona a birnin Kigali da sauran wurare da wannan a buya faru.
Ya ce ko da mutum yana wani aiki mara kyau, munin aikin za a ki ba aibata mutumin ba, dole limamai su yi hattara, domin muke hawa mumbari mu yi huduba da dai sauran wasu maganganu ko jawabai ga al’umma.
Dakta Bashir ya bayyana haka ne a ya yin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya ce babban abun da ya kamaci matasa da sauran al’umma shi ne, duk wani abu da zai kawo zaman lafiya shi ya fi kamata a bai wa muhimmanci.