Tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Gary Neville, ya bukaci kungiyar da ta soke kwangilar da ta kulla da dan wasa Cristiano Ronaldo domin hakan shi ne mafita ga dan wasan da kuma kungiyar.
Neville ya yi wannan roko ne a yayin da yake hira da manema labarai a kan dakatarwar da kociyan kungiyar Erik ten Hag ya yi wa dan wasa Ronaldo a satin da ya gabata sakamakon fita da ya yi daga fili kafin a tashi daga wasa.
- Hanyoyin Kula Da Fatar Jiki (4)
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Yi Watsi Da Ra’ayin Yakin Cacar Baka Da Manufar Kama Karya
Sai dai tun a ranar Talata dan wasa Cristiano Ronaldo ya koma atisaye tare da ‘yan was an kungiyar, bayan da aka umarce shi ya motsa jiki shi kadai a makon jiya saboda a ladabtar da kyaftin din tawagar Portugal.
Ronaldo mai shekara 37, bai yadda ya canj idan wasa ba a karawa da Tottenham a gasar Premier hakan ya sa kungiyar ba ta je da shi buga wasan da ta tashi 1-1 da Chelsea ba a filin wasa na Stamford Bridge a Premier a karshen makon da ya gabata.
Daman Ten Hag ya ce sai ya hukunta Ronaldo kan abin da ya aikata, an kuma fahimci cewar kociyan da dan kwallon sun tattauna a tsakaninsu domin dinke barakar da ake ganin ta bullo a tsakaninsu.
Ronaldo bai bari an tashi da shi a fafatawa da Tottenham, wadda ya fice daga fili tun kana tashi karawar ba, sai dai da yake ya koma atisayen, wasu na cewa watakila sun daidaita tsakaninsu da Erik ten Hag din.