Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya ce ya fitar da dan was an gaba na kungiyar Erling Haaland domin yana fama da zazzabi da kuma jin zafi a kafarsa a ranar Talata.
An sauya Erling Haaland a was an Champions League da Manchester City tatashi 0-0 a gidan Borussia Dortmund ranar Talata kuma Guardiola ya ce dole sai sunyi taka tsan-tsan da lafiyar matashin dan wasan.
Haaland ya ci kwallo 22 a wasa 15 da yafara buga wa Manchester City a kakar nan kuma dan wasan ya taba kwallo sau 13 da buga ta zuwa raga daya amma aka tare, daga baya aka sauya shi a karawar tare da Joao Cancelo.
Pep Guardiola ya ce ”Ina ganin dan wasanna bukatar hutu, yana kuma fama da dan zazzabi a tare da shi haka kuma Haaland na jin radadi a kafarsa shi ya sa ba zai iya buga zagaye na biyu ba ”Ya ci gaba da cewa ”Na yi magana da likitocin kungiyar da aka yi hutu, sun nuna min fargabarsu, amma na ga yana takawa yadda ya kamata kuma za mu auna shi sosai mu ga halin da yake ciki.
”Manchester City ta samu gurbin shiga zagayen kungiyoyi 16 da za su buga zagayen gaba har da makin da ta samu a Jamus a gasar Zakarun Turai kuma za ta ziyarci Leicester City a wasan Premier League ranar Asabar da za su fafata a filin wasa na King Power.