An gudanar da taron Maulidin Nabiy a gidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
Taron zaman Maulidin ya sami halartar dan takarar Gwamnan jihar Kano a NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusuf da sauran mutane da dama.
Sheik Muhammad Ashiru Nata’ala Babban Limamin Masallacin Mila Gidan Kwankwasiyya ya ce taro ne na murnar tunawa da fiyayyen halitta Annabi Muhammad da kuma kokarin hada kan al’umma gaba daya ya zamanto dukkan wanda ya shaida da La’ila ha’illallahu mu zama uwa daya uba daya ba kyama.
Ya ce wannan ta sa jama’a daban-daban na kowane bangare na fahimtarsa na addini ya zo Maulidin da aka asssa shi shekaru hudu kenan duk shekara ana samun ci gaba.
Sheik Muhammad Ashiru Nata’ala ya ce jagoran Kwankwasiyya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso shi ne kashin bayan assasa zaman Maulidin da aka yana bad agudummuwa sosai wajen bunkasa Maulidin ta fitar da makudan kudi da abinci da memo da ruwa wanda mutune Samara 5,000 za su amfana.
Ya yi kira ga sauran al’umma yan siyasa da wadanda ba yan siyasa ba su daure su rika koyi da irin hidimar Dokta Rabiu Musa Kwankwasodomin yana bada dukiyarsa da lokacinsa da tunaninsa a kan raya Maulidin Annabi.
Wanda har tambaya yake in wata ya kama ya ce yaushe ne za’ayi zaman Maulidinna Mila saboda son abin wannan ya nuna son sa ga addini a aikace ba’a baki ba a aikace yake nunawa.
Sheik Ashiru Muhammad Nata’ala ya ce ba abinda za suce gama halarta maulidi sai godiya Allah ya saka da alkhairi domin kowa ya tashi zuwa baya zuwa shi kadai kuma cikin gidiyar Allah yan uwa yan Shi’a da yan tijjaniya da kadiriyya da yan ‘uwana addini na kowane bangare sun zo an yi maulidi tare hatta wadanda da suke cewa ba sa son Maulidin yanzu da Kansu suke cewa a yi.