Mataimakin shugaban kwaleji nilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, Dakta Miswaru Bello ya bayyana cewa daliban kimanin 4000 ne suka shiga tsarin bunkasa noman kayan lanbona zamani, domin samar da nau’in kayayyakin lanbo iri-iri da suka hada da ganyayyaki da salat, kabeji, tumatu, karas, da sauran kayayyakin lanbo da ake noma su mai yawa a dan kankanin waje ko gona.
Cibiya HORTI NIGERIA ta zabi kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi domin ta horar da malamai a matsayi wacce za a yi gwaji na samar da kayan abunci na lanbo na tsawo shekara biyar, kamar yadda aka cimma yarjejeniya da wannan cibiya da ta zo daga kasashen Holland da Newzerland domin bunkasa noma a Nijeriya da aka zabi wasu jihohi da kananan hukumomi saboda noman zamani.
- Hanyoyin Kula Da Fatar Jiki (4)
- An Samar Da Guraban Ayyukan Yi Ga Karin Mutane Miliyan 10.01 A Kasar Sin Daga Watan Janairu Zuwa Satumbar Bana
Ya bayyana hakan a lokacin da ya wakilci shugaban kwalejin Sa’adatu Rimi, Farfesa Isah Bunkure a taron da HORTI NIGERIA ta shirya a kwaleji na ranar Talata da ta gabata.
Dakta Bello ya ce bayan sun zo wannan makaranta ta Sa’adatu Rimi sai aka zauna aka cimma yarjejeniya yadda tsarin zai tafi ta yadda su masu wannan aiki za su shigo da dalibai daga waje da na cikin kwalejin.
Ya ce karkashin wannan shirin, kimanin dalibai 4000 masu karanta harkar gona a makarantar duk sun shiga wannan shiri kuma sun gamsu da yadda tsarin yake tafiya na bunkasa samar da abunci.