An samu tashin hankali a unguwar Adeola Odeku da ke Victoria Island, a Jihar Legas bayan fashewar wani abu a wani gini da ake yi.
Ana zargin wani abu ne ya fashe a jikin wani janareta, wanda ya tayar da gobara a ranar Talata 1 ga Nuwamba, 2022.
- Kadarorina Na Sayar Na Dauki Nauyin Karatun Dalibai –Kwankwaso
- Barazanar Kai Harin Ta’addanci: Buhari Zai Gana Da Hafsoshin Tsaro Yau Litinin
Leadership Hausa ta tattaro cewa gobarar ta shafi ababen hawa da sauran gine-ginen da ke kusa da harabar.
Tuni dai jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), suka yi ta kokarin kashe wutar da ta tashi, kamar yadda aka gani cikin wani faifan bidiyo.
Cikakken bayani na nan tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp