• Leadership Hausa
Sunday, January 29, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kadarorina Na Sayar Na Dauki Nauyin Karatun Dalibai –Kwankwaso

by Abubakar Abba
3 months ago
in Labarai, Siyasa
0
Kadarorina Na Sayar Na Dauki Nauyin Karatun Dalibai –Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa ya shelanta cewa, wasu daga cikin kadarorinsa ya sayar ya dauki nauyin karatun wasu daga cikin daliban jihar zuwa karo karatunsu zuwa kasashen waje.

Kwankwanso ya sanar da hakan ne a jawabinsa a gurin taron karrama shi da kungiyar Kwankwasiyya tare da hadaka da majalisin masu ilimi suka gudanar a Abuja.

  • Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar ‘Family Support Programme’ Sun Shirya Taron Lakcoci Ga Ɗalibai Sama Da 100 A Katsina
  • Ganduje Ya Kaddamar Da Manyan Motocin Sufuri 100 Da Kanana 50 A Kano

A cewar Kwankwanso, bayan ya bar gidan gwamnatin Jihar Kano a matsayin gwamna, ya sayar da kadarorinsa da ba ya bukata domin daukar nauyin karatun daliban, inda ya nuna jin dadinsa kan yadda ya dauki nauyin karatun dalibai 3,000 da suka amfana a cikin shekaru hudu.

Ya kara da cewa, an ba shi kwarin gwiwar kirkiro daukar nauyin karatun daliban maza da mata, inda ya sanar da cewa, “bayan mun wallafa tallan na daukar nauyin karatun a 2019 mutane ‘yan kadan ne aka samu suna da babban mataki na karatu kuma mun yi amfani da su haka kuma mun yi amfani da wasu daliban masu matakin karatu na biyu wadanda su ma aka dauki nauyin karo karatunsu.

“Muna da sama da dalibai 3,000 da suka je kasashen duniya 14, saboda haka na ji dadi matuka wajen daukar nauyin karatunsu.

Labarai Masu Nasaba

Babu Wata Baraka Tsakanina Da Buhari – Tinubu

‘Yansanda Sun Kama Kasurguman ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutane 7, Sun Kwato 2.1m Kudin Fansa

“Sama da dalibai 412 ne suka amfana, inda kuma sama da 3,000 aka tura su zuwa kasar waje karo karatun.

“Ina ganin abin da ya fi dacewa ko wanne dan siyasa ya yi shi ne, ya zuba jari mai yawa a fannin ilimin zamani domin ta haka ne kawai, kasar nan za ta bunkasa.

“A lokacin ina matsayin gwamna, mun samu nasarar ciyar da daliban makarantun firamare na gwamnati na jihar.”

A nasa jawabin a gurin taron, shugaban kungiyar ta Kwankwasiyya, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya bayyana cewa, jinjina wa kokarin na Kwankwaso ne dan takarar, musamman wajen inganta rayuwar talakawa.

Tags: DalibaiDaukar NauyiIlimikanoKasashen WajeKwankwaso
Previous Post

Yajin Aiki: Gwamnatin Legas Za Ta Gana Da Direbobin Motoci Ranar Laraba 

Next Post

Da Dumi-Dumi: Mutane Da Dama Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Legas 

Related

Babu Wata Baraka Tsakanina Da Buhari – Tinubu
Manyan Labarai

Babu Wata Baraka Tsakanina Da Buhari – Tinubu

3 hours ago
‘Yansanda Sun Kama Kasurguman ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutane 7, Sun Kwato 2.1m Kudin Fansa
Manyan Labarai

‘Yansanda Sun Kama Kasurguman ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutane 7, Sun Kwato 2.1m Kudin Fansa

3 hours ago
Matsalolin Da APC Ta Jefa ‘Yan Nijeriya Ya Kamata Su Zama Darasi -Jarman Makarfi
Labarai

Matsalolin Da APC Ta Jefa ‘Yan Nijeriya Ya Kamata Su Zama Darasi -Jarman Makarfi

6 hours ago
Dole A Hada Karfi Wajen Dakile Bazuwar Makamai A Afirka –Buhari
Manyan Labarai

Ba Don A Wahalar Da Talaka AKa Sauya Kudin Nijeriya Ba —Buhari 

7 hours ago
Babu Barazanar Kai Hari A Kano – ‘Yansanda
Manyan Labarai

DPO Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Rasu A Jigawa

9 hours ago
Wasu Daga Cikin Manhajojin Da Ke Bata Wayar Android
Manyan Labarai

Wasu Daga Cikin Manhajojin Da Ke Bata Wayar Android

10 hours ago
Next Post
Da Dumi-Dumi: Mutane Da Dama Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Legas 

Da Dumi-Dumi: Mutane Da Dama Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Legas 

LABARAI MASU NASABA

Tsokaci Kan Dukan Da Wasu Maza Ke Wa Matansu

Tsokaci Kan Dukan Da Wasu Maza Ke Wa Matansu

January 28, 2023
Babu Wata Baraka Tsakanina Da Buhari – Tinubu

Babu Wata Baraka Tsakanina Da Buhari – Tinubu

January 28, 2023
‘Yansanda Sun Kama Kasurguman ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutane 7, Sun Kwato 2.1m Kudin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Kasurguman ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutane 7, Sun Kwato 2.1m Kudin Fansa

January 28, 2023
Son Rai Da Rashin Cancantar Jarumai Ke Gurbata Al’adu A Fina-finanmu –Daushe

Son Rai Da Rashin Cancantar Jarumai Ke Gurbata Al’adu A Fina-finanmu –Daushe

January 28, 2023
Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci

Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci

January 28, 2023
Bikin Bazara Na Gargajiyar Kasar Sin Ya Kara Azama Kan Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

Bikin Bazara Na Gargajiyar Kasar Sin Ya Kara Azama Kan Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

January 28, 2023
Noman Kankana Na Kara Bunkasa A Jihar Jigawa

Noman Kankana Na Kara Bunkasa A Jihar Jigawa

January 28, 2023
Masani: Sin Za Ta Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Ci Gaban Duniya A Shekarar 2023

Masani: Sin Za Ta Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Ci Gaban Duniya A Shekarar 2023

January 28, 2023
Matsalolin Da APC Ta Jefa ‘Yan Nijeriya Ya Kamata Su Zama Darasi -Jarman Makarfi

Matsalolin Da APC Ta Jefa ‘Yan Nijeriya Ya Kamata Su Zama Darasi -Jarman Makarfi

January 28, 2023
Dole A Hada Karfi Wajen Dakile Bazuwar Makamai A Afirka –Buhari

Ba Don A Wahalar Da Talaka AKa Sauya Kudin Nijeriya Ba —Buhari 

January 28, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.