Mai bawa gwamnatin jihar Borno shawara na musamman kan harkokin tsaro, Brig. Janar Abdullahi Ishaq (rtd) ya bayyana cewa kimanin tubabbun mayakan Boko Haram 3500 ne cikin sama da 80,000 da suka mika wuya tare da iyalansu ga sojoji aka mayar da su cikin al’ummominsu a jihar Borno.
Mashawarcin na musamman ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Maiduguri yayin da yake jawabi a wani taro da wasu masu ruwa da tsaki ( Peace Ambassadors Centre for Humanitarian Aid and Empowerment (PACHE) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno da British Council suka shirya.
Brig. Janar Abdullahi ya kara da yiwa inda tubabbun ‘yan ta’addan nasiha da su kasance cikin halin kirki a cikin al’ummominsu inda aka mayar dasu.
Brig. Janar Ishaq ya bayyana cewa zaman lafiya da al’umma shine koyarwa da muradin gwamnatin jihar ga tubabbun ‘yan ta’addan, inda ya kara da cewa ‘yan uwa da abokan tubabbun sun yiwa sansanonin da aka killace tubabbun kawanya a ranakun Asabar da Lahadin da ta gabata domin rungumar ‘yan uwansu da abokansu.