Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC) ta kaddamar da bincike kan aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla da aka ware kudi har dala biliyan 6 bayan kwashe shekaru har yanzun babu wani aikin da aka tabuka.
Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin wutar lantarki domin kare kasafin kudin 2023 da ma’aikatarsa ta nema.
Ministan ya ce, ma’aikatarsa ta gana da masu ruwa da tsaki kan aikin, a halin yanzu ana kan warware duk wasu batutuwan da suka hana cigaba da gudanar da aikin, inda ya ce batun shari’ar da ake yi kan aikin samar da wutar lantarkin ta Mambilla ta kawo cikas sosai kan ci gaba da aikin.
Shugaban Kwamitin Samar da Wutar Lantarki na majalisa, Gabriel Suswan, ya nuna damuwarsa kan aikin samar da wutar lantarkin, inda ya ce duk da dimbin kason da aka fitar kan aikin na tsawon shekaru, har yanzu babu wani abu da za a iya nuna wa kan Cigaban aikin.
Daga nan ne Majalisar Dattawa ta gayyaci Ministar Kudi, Zainab Ahmed domin ta yi bayani kan wani sabon kudi da aka ware cikin kasafin kudin ma’aikatar wutar lantarkin na aikin samar da wutar lantarkin ta Mambilla.