A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, a hannu guda kuma hukumomi da masana a fannin yaki da sauyin yanayi na yin gargadi game da yadda yunwa da fari da sauran bala’u daga indallahi za su iya addabar sassan duniya.
Kuma ana iya ganin haka a wasu sassa na duniya dake fama da matsaloli na ambaliyar ruwa ko mahaukaciyar guguwa dake tafe da ruwan sama da ma fari a wasu sassa na nahiyar Afirka da makamantansu.
Masana dai sun sha yin gargadi tun ma kafin bullar annobar cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba gani irinta ba, tun a lokacin yakin duniya na biyu, saboda wasu dalilai.
Na baya-bayan shi ne, kiran da hukumomin agaji da dama suka yi na gaggauta samar da karin kudade da shugabanci na-gari, don tinkarar gagarumar matsalar ayyukan jin kai dake fuskantar miliyoyin mutanen dake zaune a shiyyar gabashin Afrika sanadiyyar matsanancin fari, har ma aka yi kashedin cewa, muddin aka yi jinkiri to, babu makawa rayukan jama’a da dama na iya salwanta.
Haka ma kwararru daga nahiyar Afirka sun bukaci kasashen da suka ci gaba, da su cika alkawuran da suka dauka, na samar da isassun kudaden gudanar da ayyukan dakile sauyin yanayi, yayin taron COP27 da zai gudana a birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar.
A cewarsu kasashen da suka ci gaba ne ke fitar da kaso mafi yawa na iskar Carbon mai dumama yanayin duniyarmu, don haka ya dace su samar da kudaden rage tasirin sauyin yanayi ga kasashe masu tasowa, wadanda ke dandana kuda sakamakon rashin karfinsu na tunkarar wannan kalubale. Domin idan babu kira to me zai ci gawayi.
Ko da a watannin da suka gabata ma, kasashen Afika da dama sun sha fama da wasu daga cikin munanan tasirin sauyin yanayi, ciki har da ambaliyar ruwa a Najeriya, da fari a yankin kahon Afirka.
Saboda haka, nahiyar Afirka na fatan sauran sassan duniya za su fahimci mummunan tasirin da nahiyar ke fama da shi daga sauyin yanayi.
Idan ba a manta ba kasashe masu wadata sun yi alkawarin baiwa nahiyar Afirka gudummawar dalar Amurka biliyan 100 a duk shekara, domin gudanar da ayyukan dakile tasirin sauyin yanayi, amma har yanzu shiru ka ke ji, wai malam ya ci shirwa.
Idan har duniya na fatan magance matsalar tasirin sauyin yanayi, ya dace taron na wannan karo, ya duba alkawuran da aka yi yayin taron COP26 na birnin Glasgow, ta yadda za a fitar da kyakkyawan tsarin aiwatarwa, wanda kowa zai amince da shi. Domin kyan alkawari aka ce cikawa. Kuma wannan shi ne dattaku.
Matsalar sauyin yanayi, na kara sanya tarin jama’a kauracewa muhallansu lamarin dake sanadiyyar fadawar karin mutane cikin yanayin tsananin bukata.
Wannan ne ma, ya sa masu fashin baki ke cewa, yanzu ne lokacin da ya dace na daukar matakai, domin kaucewa fadawar miliyoyin al’ummomi, musamman dake shiyyar gabashin Afrika cikin garari. Aka ce da zafi-zafi kan bugi karfe. (Ibrahim Yaya)