A daidai lokacin da tsugunu ba ta kare ba a cikin jam’iyyar PDP, shugaban PDP, Sanata Iyorchia Ayu ya bayyana cewa yana da damar hana Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom da duk wadanda suke kiraye-kiraye ya sauka daga mukaminsa takara a zaben 2023.
Shugaban PDP ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a gidansa da ke Gboko.
- Hadin Gwiwar Sin Da Pakistan Mai Karfi Ta Haifar Da Sabbin Sakamako
- Wakilin Jaridar LEADERSHIP Ya Maka Ado Doguwa A Kotu Kan Yi Masa Mahangurba
Ortom da wasu gwamnoni biyar na PDP sun bukaci Ayu ya sauka daga mukaminsa bayan da Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP. Gwamnonin sun bayyana cewa yankin daya bai kamata ya fitar da shugaban jam’iyyar PDP da kuma dan takarar shugaban kasa ba.
Shugaban PDP ya fadi haka ne a daidai lokacin da Ortom yake takarar sanata a cikin jam’iyyar. Ayu ya siffanta kansa a matsayin uban, domin haka ba zai dakatar da wadanda suke kiraye-kirayen ya sauka daga mukaminsa daga yin takara a karkashin jam’iyyar PDP ba.
A cewar Ayu, “Na yi shiru kan abubuwan da nake ji ana cewa game da ni saboda ban san jin ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar PDP. Ina da ikon hana wane da wane yin takara saboda sai na amince wani zai iya yin takara. Amma bai yi haka ba, inda na amince duk dan takarar da PDP ta tsayar su yi takara ko ina so ko ba na so.