Koko daga kasar Ghana, shayi daga Kenya, Gahawa daga Habasha, zuma daga Zambia, barkono daga Rwanda……A cikin ’yan shekarun baya, karin kayayyakin kasashen Afirka na shiga kasuwannin kasar Sin, wadanda kuma suka samu karbuwa wurin al’ummar Sinawa.
A hakika, ba kayayyakin kasashen Afirka kadai ba, ingantattun kayayyaki daga fadin duniya na kara shiga kasuwannin kasar Sin cikin ’yan shekarun baya, wadanda baya ga biyan bukatun al’ummar kasar, sun kuma samar wa kasashen da ke fitar da kayayyakin damar cin gajiyar kasuwar kasar Sin mai matukar girma, kuma hakan na faruwa ne sakamakon yadda kasar Sin ke ta kara bude kofarta ga ketare.
Kwanan nan, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na kasa da kasa karo na biyar, ko CIIE a takaice, a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. Bikin da aka fara kaddamar da shi a shekarar 2018, wanda kuma ya kasance baje koli na farko a duniya, dake da jigon kayayyakin da ake shigo da su daga kasa da kasa.
A gun bikin kaddamar da baje koli karo na biyar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce, yau shekaru biyar da suka wuce, na sanar da shirya bikin, da nufin kara bude kofar kasar Sin, ta yadda babbar kasuwar kasar Sin za ta kasance babbar dama ga duniya baki daya. Kididdiga ta nuna cewa, a wajen bukukuwan CIIE hudu da suka gabata, adadin kayayyakin da aka baje kolinsu ya kai dubu 270, kuma jimillar darajar yarjeniyoyin da aka daddale ta zarce dala biliyan 270, inda aka bullo da sabbin hajoji, da fasahohi, da hidimomi da yawansu ya wuce 1500. Bikin CIIE, tamkar dandali ne ga kasar Sin, na kafa sabon tsarin samar da ci gaba, da fadada bude kofarta ga kasashen ketare, inda sassan kasa da kasa za su ci gajiya tare.
A halin da ake ciki yanzu na fuskantar manyan sauye-sauye a duniya, da rashin karfin farfadowar tattalin arzikin duniya, shugaba Xi Jinping a jawabin da ya gabatar, ya yi nuni da cewa, bude wa juna kofa muhimmin mataki ne da zai tabbatar da ganin ci gaban dan Adam da bunkasuwar duniya, ya ce,“Ya dace mu kara bude kofarmu, don daidaita matsalolin ci gaba, da fadada hadin-gwiwa, da kara karfin yin kirkire-kirkire, da kuma samar da ci gaba tare, ta yadda za’a kara dunkule tattalin arzikin duniya baki daya, da samar da ci gaba ga kasa da kasa, don kara amfanar al’ummominsu cikin adalci”.
Duk da cewa ana fuskantar matsalolin kariyar ciniki da ra’ayi na kashin kai, amma kasar Sin ba ta taba daina kokarinta na kafa sabon tsarin tattalin arziki dake bude kofarta ga kasa da kasa ba. A cikin shekaru 10 da suka gabata, jimillar cinikayya a tsakanin Sin da kasashen duniya ya karu daga dala triliyan 4.4 zuwa triliyan 6.9, matakin da ya sa kasar Sin ta zamanto ta farko wajen yawan yin ciniki a duniya, da ma babbar abokiyar ciniki ga kasashe da shiyyoyi sama da 140.
Kaza lika kasar ta kuma rage matsakaicin kudin kwastam da ta sanya a kan kayayyakin da ta shigo da su daga kasa da kasa, zuwa kimanin kaso 7.4%, wato kasa da kaso 9.8% da ta alkawarta lokacin shiga kungiyar WTO, tare da cire kudin kwastam kan kaso 98% na kayayyakin da take shigowa daga wasu kasashe 16 da suka fi karancin ci gaba. Baya ga haka, matakan da ta dauka na haramta fannonin da ’yan kasuwan waje suke iya zubawa jari ma sun ragu daga 190 zuwa 27, raguwar da ta kai kaso 85%……
Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin dake kan karagar mulkin kasar, a babban taron wakilanta karo na 20 da aka gudanar a kwanan baya, ta jaddada cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka a kan aiwatar da manufar bude kofarta ga kasashen waje, ta yadda kasar Sin za ta samar da damammaki ga duniya bisa ga ci gabanta, don kasashen duniya su ci gajiya.
A nan gaba, kasar Sin za ta kara bude kofarta, kuma kasar na son kasashen Afirka da ma sauran kasashen duniya su ci gajiyar damammakin da ake da su a babbar kasuwarta, da tsarinta na bude kofa da ma hadin gwiwar kasa da kasa. (Mai Zane: Mustapha Bulama)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp