Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da hakimin kauyen Kwangami, Muhammad Galadima da wasu mutane shida a karamar hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.
Wata majiya ta shaida wa Leadership cewa ‘yan bindigar dauke da makamai sun yi awon gaba da mutanen ne a ranar Litinin.
- Majalisar Dokokin Adamawa Ta Amince Da Kudirin Dokar Kafa Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
- Duniya Za Ta Dandana Kudar Matakin Da Amurka Ta Dauka
A cewar majiyar, an samu rudani a kauyen yayin da mazauna kauyen suka yi kokarin tserewa daga harin, inda suka ce mutane da dama sun jikkata.
Ya bayyana cewa an sace Hakimin da sauran mutanen daga gidajensu inda suka yi awon gaba da su zuwa daji.
Ya ce, “A halin yanzu muna rayuwa cikin tsoro saboda ‘yan bindiga a ko da yaushe suna tare da mu suna sace mutanenmu suna neman kudin fansa.
Ya bayyana cewa a kwanan baya, “sun yi garkuwa da mutanen kauyenmu guda 10 a gonakinsu. Har yanzu suna tsare sakamakon kasa biyan kudin fansa.”
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Mohammed Shehu, an kasa samun sa bare a ji ta bakinsa kan lamarin.