Kungiyar tuntuba ta dattijan arewa ta yi Allah wadai da harin da wasu ‘yan bangar siyasa suka kai wa tawagar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, a Maiduguri lokacin da yake yakin neman zabe, a jiya Laraba.
Kungiyar ta yi gargadin cewa irin wannan hari na iya haddasa rikici a kasar matukar bangaren da aka cutar ya nemi yin ramuwar gayya.
Ta dai ja hankalin ‘yan siyasa su dinga taka wa magoya bayansu burki, idan kuma ba haka ba za ta shawarci al’umma su juya musu baya, kamar yadda sakataren kungiyar Malam Murtala Aliyu ya shaidawa BBC.
In ba a manta ba dai, Kimanin mutum 74 ne aka yi zargin an kwantar da su a asibiti sakamakon harin, motoci sama da 100 aka farfasa a farmakin da yan dabar siyasa suka kai wa tawagar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a lokacin da ya ziyarci birnin Maiduguri ta jihar Borno a gangamin yakin neman zaben da jam’iyyar ta gudanar da yammacin ranar Laraba.
Sai dai, Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta karyata rahoton harin da aka kai kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a wani gangamin yakin neman zabe a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Laraba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Abdu Umar ne ya bayyana hakan ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Sani Shatambaya.
Sai dai, ya ce an kama wani mutum mai suna Danladi Abbas saboda yunkurin da ya yi na jifan ayarin motocin dan takaran a kan hanyar filin jirgin sama na Maiduguri.