Abokai, yanzu ana gudanar da babban taron yanar gizo na duniya a kasar Sin. Bunkasuwar Sin a wannan fanni ya amfanawa duk fadin duniya. Yau “duniya a zanen MINA” zai yi muku bayani kan ma’anar hadin kan Sin da Afrika a fannin tattalin arzikin yanar gizo.
Taron da ake gudanarwa a birnin Yiwu dake lardin Zhejiang ya samu halartar wakilai fiye da 2000 daga kasa da kasa, kuma babban abin da ake tattaunawa a taron shi ne hadin kai da samun ci gaba tare.
Bisa kididdigar da hukumar kula da masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta bayar, an ce, yanzu Sin ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninta da kasashe 17 dake kan hanyar siliki ta fannin yanar gizo, kuma ta kafa tsarin hadin gwiwa da kasashe 23 dake kan wannan hanya a fannin kasuwanci ta yanar gizo.
Alkaluman da kwamitin kula da sadarwa na Najeriya ya bayar, sun yi nuni da cewa, ya zuwa watan Yuni na bana, yawan mutanen dake kama Intanet ya haura miliyan 150, wato kaso 70% na al’ummar kasar na samun hidimar yanar gizo. Irin wadannan sauye-sauye da aka samu ba su rabuwa da ababen more rayuwa da kamfanonin Sin ke taimakawa wajen gina su a kasar ta fannin yanar gizo.
Cikin ‘yan shekarun baya, kamfanonin Sin sun himmantu wajen kafa na’urorin yanar gizo a Afrika. Alal misali, zuwa karshen watan Oktomba da ya wuce, kamfanin ZTE na kasar Sin ya baiwa ‘yan Afrika fiye da miliyan 400 hidimar yanar gizo, ta hanyar gina na’urorin yanar gizo.
Yanzu ana iya samun sadawar 5G a nahiyar Afrika, matakin da ya baiwa tattalin arzikin yanar gizo tushen samun bunkasuwa mai kyau, shi ya sa mutane da dama suka samu arziki ta hanyar dogaro da yanar gizo.
Wata takardar bayani kan bunkasuwar tattalin arzikin yanar gizo a Afrika da aka fitar a watan Mayun bana ta yi nuni da cewa, a shekarar 2019 yawan mutanen da suka kama ayyukan da suka shafi cinikayyar yanar gizo ya karu zuwa miliyan 233, adadin da kuma zai kai miliyan 478 kafin shekarar 2024.
Hadin kan Sin da Afrika a wannan fanni mai habaka, ya kuma ingiza cinikayyar Sin da Afrika zuwa gaba. Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, yawan kudin dake shafar cinikin bangarorin biyu ya karu da kashi 35% a shekarar bara, kuma tattalin arzikin yanar gizo ya zama sabuwar hanyar kawar da talauci a nahiyar Afirka.
A halin yanzu, kasashen Afrika da dama na sa ran yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannin tattalin arzikin yanar gizo, hakan ya sa wasu kamfanoni masu karfi na kasar Sin a wannan fanni suka hada kai da kasashen Afrika ciki hadda Najeriya, don taimaka musu wajen samun ci gaba dangane da tattalin arzikin yanar gizo a fannin hada-hadar kudi da ciniki ta yanar gizo da sufurin kayayyaki da sauransu.
Nahiyar Afrika na da kasashe maras ci gaba mafi yawa a duniya, kuma yadda kasar Sin ta ba da taimakon ingiza bunkasuwarsu bisa hadin gwiwar tattalin arzikin yanar gizo, ba shakka zai samar da sabbin damammaki masu kyau ga nahiyar wajen kawar da talauci, baya ga haka zai ingiza bunkasuwar tattalin arizkin duniya gaba daya. (Mai zane kuma rubuta: MINA)