A ci gaban tattaunawar da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi da fitacciyar Jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, kuma me taka rawa a cikin shirun Dadin Kowa wato HAJIYA SADIYA LAWAN MUSA wadda aka fi sani da SABUWAR MALAM AYUBA. Ta bayyana irin sa’ar da ta yi a masana’antar fim wadda take ganin babu kamarta. Ko me ya sa ta fadi hakan? Ga dai ci gaban tattaunawar kamar haka:
Bayan harkar fim da kike a yanzu, shin kina wata sana’ar ne?
Toh! Alhamdulillahi ina sana’o’i ma ba sana’a daya ba, tunda ni tun asali ba mace ba ce da take zama haka, ban saba zama haka ba, tun kan ma na fara fim ina sana’o’ina, in ta kama hakk dai harkoki ma kala-kala, kin san harkar mu na Mata, baya wuce kayayyaki na kwari, sannan kuma duk abin da yakama duk abubuwan da Mata suke bukata haka dai za ka dauko ka rinka siyarwa ana siya. Wasu lokutan ma har abin da za a ci ma ina sarrafawa, su abincin sayarwa haka dai a gida ko wani abu na sarrafawa wani zubin na bayar a fitar mun da shi, duk dai ina yi. Amma yanzu abin da ya fi karfi a sana’a ta shi ne sabulu, ina hada sabulun wanka Molato shi nake yi yanzu, ina hada sabulu da Mai, Alhamdulillahi kuma ya karbu har Nija ake kai mun kayana, daga can ma ana nema, don sun karbu sosai a can.
Mu dan koma baya kadan cikin shirin Dadin Kowa wanda ya fito a kanin Raliya da wanda ya fito a matsayin danki wato Dan Asabe, wasu na ta jita jitan cewa yaranki ne, me za ki ce akan hakan?
Ga baki dayansu dai ba wanda na haifa a cikinsu, duk aiku be ya hadani da su, shi wannan dan gidan Malam Barau kanin Raliya wannan katon nan, duk aikin ne ya hada ni da shi, shi ma kuma Dan Asabe mutumin Adamawa ne, aiki ne ya hada ni da shi, amma mutane da yawa suna tambayata ni kaina suna cewa ko ni na haife shi, tun da an ga yanayi kamar shi ma yana da hasken fata, ana tunanin kamar ko dana ne, duk aiki ne ya hada ni da su.
Wa kika fi so a hadaki da shi ko ita a matsayin ‘yar ki ko danki?
Ai ni ba zan iya cewa ga wanda na fi so a hadani da shi ba, na yi ‘ya’yan da yawa, kin ga a haka ma a wasu fina-finan ma Daushe kan shi ya fito a dana, su me sana’ar nan duk sun fito a ‘ya’yana, Matan kuma na taba yin ‘ya da Hadiza Gabon, na yi da Fati Washa, su Hafsat Barauniya, duk yawanci duk sun fito a ‘ya’yana, kin ga kuwa ni kowa ma, duk wanda dai ya dace a hadaka a fim, kawai shikkenan sai ka ja rol, ba matsala.
Ko akwai wanda ya taba ko ta taba bata miki rai cikin masana’antar?
Wallahi ba kowa, ni dai ina ganin ma a cikin masana’antar ba wanda ya yi sa a dai Allah na tuba irina, tun da ni dai kowa dai wallahi muna zaman lafiya da su ni ban san dalilin hakan ba, da manya da yara da Maza da Mata ni dai in dai na fita aiki ko muka hadu a wajen wata sabga na harkar ‘yan indostiri za ki ga kowa faran faran muke da shi, ban taba fada da kowa ba, shiyasa ko a cikin kannywood din ma, ina ji da kunne na ana yabona, ana cewa ina da mutunci, mutane suna taka tsam-tsam da shiga harka ta, saboda sun ganni ba ni da hayaniya, ba ni da yawan magana, indai na je waje kawai zan zauna nayi shuru, abin da ya kaini shi zan yi in an gama in tashi na tafi gida, kuma ban yaho, bana bin kawaye, ba ni da wasu kawaye na harkoki haka daban-daban, ni dai buri na in an kirani aiki da na zo na yi alla-alla nake na yi maza na koma gida wajen ‘ya’yana, wallahi haka nake a indostiri.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?
Babban abin da ya taba faruwa da ni na farin ciki ta dalilin harkar fim din nan, lokacin Nes lebil, lokacin da Shugaban Kasa Buhari za a yi wancen zaben da suka hau, lokacin an yi salaktin da ni a ciki, wanda za su je Bila, a je kamfen din Buhari muka je kuma mun samu kudi ba laifi, an ba mu makudan kudi a lokacin gaskiya shi ne na yi farin ciki sosai har kasa bacci na yi.
Me ya fi saurin saka ki farin ciki, me kuma ya fi saurin bata miki rai?
Abin da ya fi saurin sakani farin ciki shi ne na ji ni cikin kudi, wanda ya fi bata mun kuma shi ne saba alkawari.
A gaba daya fina-finan da kika yi wanne fim kika fi so wanda ya zama bakandamiyarki?
Shin din dana fi so shi ne fim din Juda.
Takaitaccen fim ne ko me dogon zango ne (series film)?
Takaitaccen film ne na RK studio
Wanne irin abinci da abin sha kika fi so?
Na fi son Wake da Shinkafa da Manja da Yaji da Salad. Abin sha kuma Zobo.
Wanne irin kaya kika fi son sakawa?
Na fi son Doguwar riga.
Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga harkar fim da ma na ciki baki daya?
Ina so na ba da shawara ga wadanda suke cikin wannan harkar da da kuma wadanda suke kokarin shigowa cikin wannan harka tafim, akan in za su shigo ciki su dauke ta a matsayin sana’a kumk su riketa da zuciya daya, sannan kuma su ruke gaskiya a cikinta, shawarata kenan.
Ko akwai wani kira da za ki yi ga gwamnati game da cigaban masana’antar Kannywood?
Ina kira ga Gwamnati ta jiha da ta tarayya akan ta tsaya ta dubi harkar nan ta fim ba kananan mutane bane suke cin abinci a cikin wannan harka, yara Maza da Mata da iyaye magidanta, ba karamin ci gaba suke samu na taimako a cikin wannan harkar ba, masana’anta ce babba, wadda daruruwan mutane suke cin abinci a cikinta, ya kamata a ce gwamnati ta zo ta tsaya ta duba harkar nan, ta tallafa ta taimaka, saboda a cikinmu ma haka dai akwai iyaye gajiyayyu suna da ‘ya’ya da yawa da Mata, amma kuma sai ka gani fim din ma ba ruke su yake ba, tun da wani lokacin sai aiki ya ya samu ai sannan za a biya mutum, ba kamar aikin gwamnati ba ne da duk wata ko kayi ko baka yi ba za a baka kudinka, toh ya kamata su rinka shigowa ana tattaimakawa da yaran da manyan gaba daya.
A ciki kuma akwai wanda suke bukatar Aure ba su da kudin da za su yi, toh kin ga da ace gwamnati za ta rinka shiga cikin harkar a kungiyance za a samu a rinka solbin din irin wannan matsalolin, saboda a haka ma akwai yara da yawa Maza da suke so su yi aure ba su da karfin da za su yi, akwaiMata ma da suna zaune suna so su yi auren, ko zawarawa ko ‘Yan Mata, amma iyayensu ba su da karfin da za su taimaka musu na kayan daki, da kuma abin da za su dan samu su zauna gidan miji na sana’a, shiyasa za ki ga wani lokacin abin yake juyawa ya koma wata sigar daban.
Me za ki ce ga masoyanki?
Toh masoyana gaba daya ina yi musu fatan alkhairi, Allah ya bar zumunci da kauna.
Me za ki ce da wannan shafi na Rumbun Nishadi da kuma ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa?
Ina yi wa wannan shafi na Rumbun Nishadi da kuma Jaridar LEADERSHIP Hausa, fatan alkhairi, ina mika godiya ta sosai a gare su, sannan kuma ina fatan Allah ya kara daukaka su.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina gaishe da al’ummar musulmi gaba daya na fadin duniyar nan, kuma ina yi musu fatan alkhairi.
Muna godiya ki huta lafiya
Ni ma na gode