Rundunar ‘yansandan Jihar Neja ta kwato shanu akalla 500 da babura takwas da ‘yan bindiga suka kwace a yayin wata musayar wuta da suka yi daga wasu kananan hukumomi uku na jihar.
Kananan hukumomin sun hada da Paikoro, Munya da Wushishi.
- Kurar Sauya Fasalin Kudi: ‘Mahaukatan’ Sayen-sayen Da Masu Boye Kudi Ke Yi
- Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Kan Tattalin Arzikin Zamani Ya Baiwa Afrika Damammaki Masu Kyau
Rundunar, a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya sanya wa hannu, ta ce jami’an rundunar sun samu nasarar dakile dukkanin hare-haren.
Ya ce a ranar Laraba wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai farmaki kauyen Kaffin-Koro da ke karamar hukumar Paikoro, ta kauyen Adunu, inda suka rika harbe-harbe ba tare da bata lokaci ba, kuma a cikin haka ne wasu mutane biyu suka samu raunuka harsashi yayin da aka yi awon gaba da wasu shanu.
‘Yan bindigar sun yi watsi da shanun da aka sace, yayin da aka kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Janar na Kaffin-Koro kuma suna karbar magani”.
A cewar rundunar ‘yansandan a ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba daga garuruwan Akare, Jiwawa, Gulanji, Kadaura, da wasu kauyuka da ke makwabtaka da Wushishi suna kokarin tsallakawa hanyar Tegina zuwa Zungeru tsakanin kauyukan Garun-Gabas da Yakila.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ‘yansanda d sojoji sun hada kai tare da mayar da martani cikin gaggawa inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.
“Sakamakon haka ‘yan bindigar sun yi watsi da shanun da suka sace da wasu babura a yayin da suka shiga cikin rudani domin tsira da raunukan harbin bindiga a dajin.
Abiodun ya kara da cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari kauyen Chibani ta gundumar Kuchi ta karamar hukumar Munya, yayin da jami’an ‘yansanda da jami’an ‘yan banga suka tattaru zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.
Ya kara da cewa, “An samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar, inda suka yi watsi da shanun, yayin da suka tsere ta Kauyen Rishi Kaduna.
Sai dai wasu mutane biyu daga cikin ‘yan banga na yankin sun rasa rayukansu a yayin artabu da bindigar.”