Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce hukumar kiwon lafiya ta Sin, ta gabatar da matakai 20, na kara kyautata ayyukan kandagarki da yaki da cutar COVID-19. An kuma fitar da wadannan matakai ne domin ayyukan yaki da cutar su kara dacewa ya ilimin kimiyya yadda ya kamata.
Ya ce matakan ba za su sassauta ka’idojin kandagarki da na shawo kan annobar ba, maimakon hakan za su inganta ka’idojin da ake bi ne, bisa yanayin sauyawar kwayoyin halittar cutar, wanda hakan ya zama dole, ya kuma dace da ilimin kimiyya.
Zhao Lijian, ya yi wannan tsokaci ne a yau Juma’a, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da wani dan jaridar waje ya yi masa tambaya mai alaka da batun.
Zhao ya kara da cewa, “Game da zirga zirgar jiragen sama, da tafiye-tafiyen ‘yan yawon bude ido, bayan Sin ta fitar da wadannan matakai, za a samu kyautatuwar sufuri, kuma matakan za su karfafa gwiwar ‘yan kasuwa wajen zuba jari a Sin. (Saminu Alhassan)