Wasu daga cikin jaruman fina-finan Nollywood da Kannywood sun isa Jos babban birnin Jihar Filato domin mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Ahmed Bola Tinubu da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima baya.
Jam’iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zabenta na shugaban kasa a Jos domin neman goyon bayan ‘yan Nijeriya su zabi Tinubu da Shettima a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa.
- 2023: Ko Takarar Gwamnan Kano Ta Yi Wa Sadiq Aminu Wali Girma?
- Gobara Ta Kone Shaguna 15 Da Lalata Kaya Na Miliyan 19 A Jihar Kwara
Wasu daga cikin jaruman Nollywood da Kannywood da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ta hango sun hada da; Jide Kosoko, Gentle Jack, Sani Mu’azu Foluke Daramola da Ali Nuhu.
Sauran sun hada da; Zack Orji, Said Balogun, Taiwo Hassan, Bimbo Akintola da sauran tarin jarumai.
Jide Kosoko, a takaice, ya ce sun je Jos ne domin nuna goyon bayansu ga Tinubu wanda ya ce yana da karfin tinkarar kalubalen kasar nan.
Koso ya bayyana cewa Tinubu ya nuna bajintarsa a duk mukaman da ya rike.
Ali Nuhu wanda ya yi magana a madadin Kannywood, ya nemi goyon bayan yan Nijeriya ga Tinubu da Shettima.
Nuhu ya bukaci wadanda har yanzu ba su karbi katin zabe ba da su yi hakan domin samun damar kada kuri’unsu.
Jarumin ya ce za su yi duk abin da ake bukata don zaburar da mambobinsu da magoya bayansu ga zabar Tinubu da Shettima.
“Ina nan tare da wasu takwarorina kuma mun zo ne domin mara wa Tinubu baya,” in ji shi.
’Yan wasan sun yi ta raye-raye da wake-wake daban-daban domin nuna goyon bayansu ga ’yan takarar APC.
NAN ta kuma rawaito cewa wasu mawaka da suka hada da Terry G, Zulezu da sauransu sun taka rawa a wajen taron.