Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa wani fitaccen shugaban ‘yan bindigan daji mai suna Kachalla Gudau, wanda ke jagorantar ayyukan ta’addanci a kananan hukumomin Chikun da Kachia da Kajuru na jihar na daga cikin ‘yan bindigar da sojoji suka kashe a Kankomi a ranar Lahadin da ta gabata.
Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa, wata majiya mai tushe daga cikin mazauna yankunan ne suka tabbatar da cewa, Gudau na daya daga cikin wadanda sojojin suka bindige yayin musayar wuta a wani harin da suka kaiwa sojojin wanda Gudau din ya jagoranta da kansa, wannan “ya kawo karshen mulkin jahilcinsa na zalunci da ta’addanci”.
Aruwan ya ce an tsinto gawar dan ta’addan, wanda aka ce yana da alaka da shugabannin ‘yan bindigar dajin da ke addabar fadin jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, a dajin Kankomi inda ya mutu.
A cewar Aruwan, majiya mai tushe ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga da dama da ke karkashinsa ne suka binne shi a wani wuri da aka ce yana kusa da dajin Kaku da ke yankin Kaso a karamar hukumar Chikun.
“Matsananciyar satar shanun sa ta zo ne a zangon farko da na biyu na shekarar 2022, inda a karamar hukumar Kajuru kadai Gudau da abokan ta’addancinsa suka yi awon gaba da shanu 1,600 da wasu 3,332, a watanni shida na farkon shekarar 2022 kadai ya sace shanu 4932. “