Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a daren ranar Talata a unguwar Maikatako da ke gundumar Butura ta karamar hukumar Bokkos, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 11 tare da jikkata wasu mutane takwas.
A wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Jihar, Makut Machan ya fitar, Lalong ya bukaci jami’an tsaro a jihar da su kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin gurfanar da su a gaban kuliya.
- Sin Za Ta Kara Raya Sana’o’in Dake Shafar Kasuwar Sinadarin Carbon
- Dakarun Soji A Jihar Kaduna Sun Kara Kashe Wani Jagoran ‘Yan Bindiga Gudau Kachalla
Gwamnan wanda ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta bari ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga su kai hari a wani yanki na jihar ba saboda an umarci dukkanin hukumomin tsaro da su tabbatar da ta yi maganin duk wani mutum ko kungiyar da ta kai harin. .
A cewarsa, yawaitar hare-hare da lalata amfanin gonaki, dabbobi, da sauran dukiyoyi a karamar hukumar ta Bokkos, na zama abin damuwa, kuma dole ne a duba su cikin gaggawa.
Wasu da ake zargin makiyaya ne sun afkawa al’ummar yankin da misalin karfe 11 na daren ranar Talata, inda suka kona gidaje hudu a harin, sannan suka fara harbi ba kakkautawa bayan da suka mamaye ‘yan banga da ke sintiri.
An ce guda tara daga cikin wadanda abin ya shafa an kona su ne ta yadda ba za a iya gane su ba a wani waje, yayin da sauran kuma aka same su da sanyin safiyar Laraba a gidajensu da suka kone bayan an harbe su.
Wani dan unguwar ya tuna cewa harin ba gaira ba dalili ya fara ne bayan ranar kasuwar Litinin ta mako-mako inda aka harbe wani yaro a Hilltop, wanda ke da tazarar kilomita daga Maikatako.
Rahotanni sun ce lamarin harbin ya haifar da tashin hankali a tsakanin al’ummar a ranar Talata duk da cewa ‘yan banga sun yi kokarin fatattakar maharan.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Filato, Alfred Alabo, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayanin lamarin ba.
Sai dai kwamandan rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo-Janar Ibrahim Ali, ya bayyana cewa rundunar tsaron da aka bai wa alhakin kula da al’amuran tsaro a Filato, da kuma wasu sassan jihohin Bauchi da Kaduna, sun kasance a kasa don shirin ko ta kwana.