Shugaban Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce akwai bukatar sauya fasalin Naira duk bayan shekaru takwas kamar yadda doka ta tanadar.
Bawa ya bayyana fatan cewa Dalar Amurka za ta ragu zuwa N200 sakamakon sauya fasalin Naira da ake shirin yi.
- Sin Za Ta Kara Raya Sana’o’in Dake Shafar Kasuwar Sinadarin Carbon
- Xi Jinping Ya Gana Da Babban Sakataren MDD
Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a wata hira da Sashen Hausa na DW a ranar Laraba.
Ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da sauya fasalin kudin Naira.
Bawa ya ce akwai bukatar sauya fasalin Naira duk bayan shekara takwas.
Ya ce, “Doka ta ce a sauya fasalin takardar kudin Naira duk bayan shekara takwas, amma mun shafe shekaru 20 ba tare da wani canji a kansu ba.
“Kuma hakan ya haifar da kashi 85 cikin 100 na kudaden da suke yawo ba a bankuna ba; a lokacin da CBN ya zo da wannan gyara, Dala ta koma N880, daga baya ta koma N680 ko kuma wani abu mai kama da hakan.
“Don haka ka wannan sauya fasalin, na iya karya darajar Dala ya fadi sosai, wanda kila ta koma zuwa N200.”
A ‘yan makonnin da suka gabata, Naira na kara faduwa a kan manyan kudaden duniya.
Naira ta sake samun tagomashi daga baya a kasuwannin musayar kudi zuwa N730 kan kowace Dala daya a makon jiya.