Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce dakarunta da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma sun kashe ‘yan ta’adda 29, sun cafke wasu 10 masu taimaka wa ‘yan ta’addan sannan kuma sun kwato tsabar kudi har naira miliyan N15,589,000.00 cikin makonni biyu.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, wanda ya bayyana hakan a wajen taron manema labarai da hedikwatar ke shiryawa duk makonni biyu kan ayyukan sojojin Nijeriya, tsakanin 3 zuwa 17 ga watan Nuwamba, 2022, ya kuma ce ‘yan ta’adda 250 ne suka mika wuya, yayin da aka ceto mutane 60 daga hannun ‘yan ta’addan.
Ya kuma tabbatar da cewa, rundunar sun kashe Malam Ali Kwaya, wani jigo a rundunar ISWAP da kuma Malam Bukar Mainoka a yayin wani farmakin da jiragen yakin sojojin sama suka kai musu.
Dangane da ayyana ‘yan ta’adda 19 da rundunar ta yi tana nema ruwa a jallo a baya-bayan nan, ya ce kudurin ya fara haifar da sakamako mai kyau.