Tun bayan rubutun da ya gabata a wannan filin na Kimiyya da Fasahar Sadarwa, akan yadda mutum zai kare kansa daga masu kwacen Facebook da WhatsApp (Hackers), to har yanzu wasu suna kiran waya a kan wannan matsala, duk da sun saka makullan sirri masu sarkakiya.
Eh lallai babu shakka zuwa yanzu yawaitar kwacen shafin Facebook da WhatsApp din ya yi sauki kadan. Amma har yanzu ana samu kadan-kadan. Ko da kuwa ka saka makullan sirri (password) masu sarkakiya, to za su iya kwace maka shafin naka ta hanyar Phishing.
- Adabin Zamanin Da Na Sin (3)
- Ana Baje Kolin Shirye-Shiryen CMG A Taron Kafofin Watsa Labaran Kasa Da Kasa Karo Na Farko
Menene Phishing?
Phishing wani tarko ne wato wani ‘common technikue’ ne wanda ake amfani dashi wurin kwacen makullan sirri na Facebook da WhatsApp (hacking password) har da asusun ajiya na Banki.
Phishing wata manhaja ce wadda ake cracking da copy na sirrukan masu website, page, da kuma sace wa users password, da labarai masu muhimmanci (sensitibe information) kamar katin waya (credit card) da sauransu.
Daga cikin hanyoyin da ‘hackers’ din suke bi don kutse a shafukan mutane, har su kwace shafin ta hanyar Phishing shi ne, suna kirkirar ‘page’ na bogi, wanda ya yi kama da wani shafi na gaskiya. Wato za su kwaikwayi wani shafi su yi ta yada shi (sharing). Da farko suna dubawa su ga me aka fi damuwa da shi, to sai su bude shafi mai kama da wancan din. Kuma sun fi bude shafi mai alaka da daukar ma’aikata, wanda zai samu tururuwar cike-cike na jama’ar.
Mu dauki misali da shafin INEC na daukar ma’aikata da shafin N-Power. Masu kutsen ‘Hackers’ sun bude page a Facebook da website daban-daban duk na bogi da sunan N-Power. Jama’a da dama sun yi rubdugu da tururuwa wajen bin wadannan shafuka, a tunaninsu shafin N-Power ne na gaskiya. A cikin wadannan shafukan nasu, za su ce ka saka email da password har da lambar waya. Wani lokacin har da lambar BBN suke tambaya. Ta haka za su samu bayananka (details), sai ya zama duk shafukanka na Facebook, whatsapp da asusun ajiyarka na Banki da sauransu duk za su iya kutsawa su shiga.
Mafi yawan mutane ana yaudararsu ne ta hanyar a yi musu abu kyauta (free). Masu Phishing suna kikirar shafin bogi na MTN, Airtel, ko Glo, sai suce ka saka email da password dinka za a baka kyautar “1GB ko 3GB data”. Da zarar ka saka shikenan sun samu bayananka, sai su yi abin da suke so yi da shi. Su kuma mafi yawan mutane suna da son abu na kyauta, to anan kuma, ake rasa muhimman abubuwa.
Kwanan nan hackers din suka yi amfani da manhajar Phishing suka kikiri wani shafin N-Power na bogi a WhatsApp, sai suce ka saka lambar wayarka, idan ka samu N-Power za su sanar da kai. Kowa idan ya saka, to ya samu. Sai su taya ka murna. Sai su ce ka tura a group din WhatsApp guda biyar. Duk abin da ka ji an ce maka ka tura a group biyar ko sama da haka. Kai ko a group daya aka ce ka tura, wannan shafin na bogi ne.
Akwai wani misali da wani ya bayar a kan irin yadda mutane suke son abu na kyauta.
Ya ce “akwai wani mutum ya gina gidan namun Daji (Zoo), sai yace kudin shiga Naira dubu biyar (5,000). Amma mutane suka ki shiga. Ya rage kudin zuwa dubu Hudu (4,000) nan ma dai aka ki shiga, sai ya sake rage wa zuwa zuwa dubu biyu (2,000) a hakan ma aka ki shiga”.
To sai ya yi wata dabara, yace “duk mai son shiga ya zo ya shiga kyauta” ai nan da nan gidan ‘zoo’ din nan ya cika makil da mutane. Sai kawai ya je ya kunce Zaki. Ai kuwa jama’a suka yi ta gudun ceton rai, kowa yana kokarin fita. Sai yace “duk mai son fita, sai ya bada dubu Goma (10,000), haka aka yi ta biyan dubu goma-goma ana fita. To ka ga irin halin da masu son abu na kyauta yake jefa su.
Idan har za ka yi amfani da wayoyin nan na zamani, to ka kiyaye duk wani abu da aka ce na kyauta ne. Ko ka ga wani shafi an ce maka ana daukan ma’aikata, to ka yi kwakkwaran bincike kafin ka cika.
Abu muhimmi da mutum zai kiyaye shi ne, duk abin da aka ce maka ka saka email, password, lambar waya, lambar asusun ajiya, NIN number, da lambar BBN, to ka yi kwakkwaran bincike, bincike mai zurfi fa sosai, don wadanda suka daukar wa kansu wannan sana’a ta kutse a asusun ajiyar mutane da kutse a shafukan sada zumunta na mutane kullum suna kara fito da sabbin dabaru.