A ranar Talata ce, jam’iyya mai mulki ta APC ta fara gudanar da yakin neman zabenta a garin Jos Babbar Birnin Jihar Filato, domin tallata jam’iyyar ta yadda ‘yan Nijeriya za su sake zabenta a 2023.
Kamar yadda yakin neman zaben 2023 ya kankama, hankulan jam’iyyun siyasa da masu neman takara ya kamo kan tallata manufofinsu a kakafen sadarwa ta yadda za su saye zuciyar masu jefa kuri’a har ma su zabe su.
- Masu Cutar Sikari Na Fuskantar Karin Kudin Magani Da Kashi 200
- Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Tsige Fadah A Matsayin Darakta Janar Na NYSC
Sashe na 94 (1) na dokar zaben 2022 ya bai wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) daman dage takunkumin yakin neman zabe tun a ranar 28 ga watan Satumbar 2022.
Bisa tsarin dokar zaben 2022, wannan shi ne karo na farko da kasar nan ta samu damar gudanar da yakin neman zabe har na tsawon watanni biyar, inda a baya ayyukan jam’iyyun siyasa na gudanar da yakin neman zabe ya yi karanci.
Kafin dai hukumar INEC ta dage takunkumin fara yakin neman zabe, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da sauran wasu gwamnoni da ke cikin jam’iyyar sun yi zawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin samun goyon bayansa a babban zaben 2023.
Tinubu tare da mataimakin takararsa, Sanata Kashim Shettima da gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun da AbdulRahman AbdulRazak na Jihar Kwara da Bello Matawalle na Jihar Zamfara da gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru da kuma gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong wanda shi ne darakta janar na yakin neman zaben jam’iyyar duk suna daga cikin wadanda suka gana da Jonathan.
Haka kuma tsohon gwamnan Jihar Legas ya ziyarci tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a Abeokuta da tsofaffin shugabanin kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida da kuma Janar Abdulsalam Abubakar.
Tun da farko dai, jaddawalin ayyukan yakin neman zaben APC an dakatar da su ne bayan da aka samu rudani kan jerin sunayen mambobi 422 na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa.
An dai yi tsammanin cewa jam’iyyar ta samu nasarar dinke barakar wanda aka sake fitar da jerin wadansu sunaye na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da kowa ya amince da shi.
Bayan an samu nasarar lallashin ‘ya’yan jam’iyyar da suka fusata, Shugaban Kasa,
Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC tare da amincewa da a zabi Tinubu domin ya gaje shi.
Ya ce zaben Tinubu zai karfafa nasarar da gwamnatinsa ta samu a matsayinsa na dan takara mai nagarta da kyakkyawan shugabanci wanda zai iya dorawa daga wurin da suka tsaya.
Bayan kaddamar da kwamitin yakin neman zaben, an dai samu karancin gudanar da yakin neman zabe a cikin jam’iyya mai mulki wanda ba a yi tsammanin hakan ba. An dai bayyana cewa dalilin da ya sa aka samu tsaikon dai shi ne, mafi yawancin daraktocin yakin neman zaben sun dokara ne da kasafin kudi na gudanar da lamarin. Sannan an bayyana cewa lokacin da aka kammala kasafin kudin, za a saki kudaden ga daraktocin nan take domin gudanar da harkokin yakin neman zabe.
Jam’iyyar APC ta fara gudanar da yakin neman zabenta ne a garin Jos Babban Birnin Jihar Filato a ranar 15 ga watan Nuwamba gabanin zaben 2023. Jam’iyyar ta gana da kungiyoyin manoma a Jihar Neja a ranar 7 ga watan Nuwamba, sannan ta kara wani ganawar irin wannan da kungiyar masu hakar ma’adanai a ranar 9 ga watan Nuwamba a Keffi na Jihar Nasarawa.
Jam’iyya mai mulki ta sake gudanar da irin wannan tattaunawa a Kalaba na Jihar Kuros Ribas a ranar 12 ga watan Nuwamba na yadda za ta fara gudanar da yakin neman zabe a garin Jos ranar 15 ga watan Nuwamba. Wannan yana zuwa ne bayan tattaunawa a Jihar Imo ranar 17, inda daga bisani ta gudanar da ganganminta a Jihar Delta ranar 19 ga watan Nuwamba.
Da yake jawabi a ranar Alhamin da ta gabata lokacin kaddamar da kwamitin tuntuba na yankin arewa maso yamma karkashin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Darakta Hon. Aminu Jaji ya bayyana cewa jam’iyyar ta cancanci yakin neman zabe mai tsari da zai bambanta da na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPPA, Rabi’u Kwankwaso da ke yankin arewa maso yamma.
A cewarsa, wannan lokacin ne da za a saka wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da kuma mutanen yankin kudu maso yamma bisa yadda suka goyi bayan Shugaban Kasa Buhari a zabukan 2015 da 2019.
Jaji ya ce bisa goyon bayan Shugaba Buhari na tsawan mulkinsa shekara bakwai da rabi, yankin arewa maso yamma zai goyi bayan samun nasarar Tinubu/Shettima a zabe mai zuwa.
Ya dai bukaci mambobin kwamitin yakin neman zabe su yi aiki tukuru wajen ganin samun nasarar jam’iyyar APC a kowani mataki a kasar nan.