• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sirrin Sarrafa Dankali Da Karas

by Bilkisu Tijjani
3 years ago
Karas

Sau tari mutane sun dauka cewa duk abin da ya shafi nau’ukan abinci sai dai a ci kawai, amma a hakikanin gaskiya masana da dama na bangaren kiwon lafiya sun fitar da nazarurruka masu inganci a kan amfanin kayan abinci wajen kiwon lafiya da abubuwa da dama da suke da amfani a jikin dan adam.

Hakan kuwa ta sa wannan shafi ya taso gadan-gadan don ya tabo bangarori da dama, wadanda suka shafi harkokin tattalin kai, gyaran jiki da dukkanin tanadin da mace ke bukata wajen inganta rayuwar aurenta.

  • Masu Cutar Sikari Na Fuskantar Karin Kudin Magani Da Kashi 200
  • ‘PHISHING’ Sabuwar Hanyar Kutse A Facebook, WhatsApp  Da Asusun Ajiyar Banki

Wadanda ke biye da mu, sun amfana da abubuwa masu yawa kan abin da ya shafi dukkanin abubuwan da muka ambata a sama. Kan haka ne, na ga dacewar kara lulawa cikin darasin. A wannan makon za mu dora ne daga inda muka tsaya.

Masana harkar kiwon lafiya sun yi bayanai dangane da muhimmancin kula da jiki kamar yadda na yi shimfida a farkon rubutun nan, musamman ga mata domin halittar mace daban yake da namiji. Matukar mata ba sa kula da jikinsu, babu shakka za su wayi gari, hatta ‘yan kananan ayyukan gida ba za su iya ba, ballantana kula da yara, uwa uba kuma gyaran dangatakan aurenta.

Za mu dan tattauna kan wasu ababen da za a iya amfani da su domin warkarwa ko kare kai daga kamuwa da wadansu cututtukan da suka shafi cutar daji, wato CANCER.

LABARAI MASU NASABA

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

Cututtukan da sinadarin ke warkarwa, bayan ciwon daji, sun hada da:

  1. Cututtukan da ke kusantar hanta da koda
  2. Yana warkar da cutar gyambon ciki, wato ULCER
  3. Yana tsafatace huhu
  4. Yana kare mutum daga kamuwa da ciwon zuciya da hawan jini
  5. Yana wanke idanu (jajaye da busassun idanu).
  6. Yana taimakawa wajen kare masu motsa jiki daga matsalolin jijiya
  7. Yana warkar da zazzabin jiki
  8. Yana gyaran fatar jiki ya yi kyau sosai, ko da kuwa mutum yana fama da kuraje a fuska da jiki.
  9. Yana kawar da gyatsa ko numfashi mai wari daga baki.
  10. Ya na rage ciwon mara ga mata
  11. Haka kuma yana rage kiba matukar ragewa inda za a yi amfani da shi daidai bisa tsari.

Idan muka kalli wadannan cututtuka, wa la Allah a yi tunanin maganin sai masu kudi za su iya sayensa. Ma iya cewa kyauta ce daga Allah, magani ne da komin talaucin mutum zai iya sayensu. Abubuwa guda hudu ne a ke amfani da su wajen hadin maganin, su ne kamar haka:

Karas

Dankalin Hausa

Tuffa (Apple)

Lemun tsami.

Abu na farko da za mu yi shi ne, mu fere dankalin, bayan nan sai mu yi amfani da wuka mai kaifi wajen rede bayan Tuffa dinmu, mu kankare bayan Karas din. Bayan an gyara wadannan, sai a yi amfani da na’uran zamani mai markada kayan miya da kayan marmari a markada su daidai kamar yadda a ke matse lemo. Idan babu na’uran zamani irin Blender ko Juicer, sai mu yanyanka su kanana, har sai ya zama tamkar madarar lemo, mu yi amfani da dukkanin dabarun matse lemo domin sha.

Bayan an markada, sai a tace shi sosai, sannan a shanye shi lokaci guda. A kula, nan fa ba sai an sanya cikin Fridge ba. An fi so a shanye shi lokaci guda domin hakan ke sanya maganin aiki cikin sauri. Yanayin shan kuma yana tsari mai inganci. An fi son a sha maganin kafin karin kumallo. Kuma a bada akalla sa’a guda tsakanin shan maganin da cin abinci. Misali, idan mutum yana karin kumallo da karfe tara na safe, sai ya yi kokarin shan maganin da misalin karfe takwas daidai. Wannan ita ce ka’idar farko. Ka’ida ta biyu kuwa, tilas a bi tsarin hadin maganin, kamar yadda muka tattauna a baya.  Allah Ya ba da sa’a.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Tsaro

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Next Post
Shugaba Xi Da Uwargidansa Sun Gana Da Sarki Da Sarauniyar Thailand

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025
Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.