Yayin da ta ke ta shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na sanatoci, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce ta yi shirin gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa a 2023 idan hakan ta kama.
Kakakin INEC Festus Okoye ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da editocin jaridu da wakilan kafafen yaɗa labarai a Abuja.
Ya ce dama a bisa al’ada, INEC na yin irin wannan shiri a duk lokacin da za a yi zaɓen shugaban ƙasa, tun daga 1999.
Okoye ya ce a irin wannan shiri, tun da farko dai INEC za ta ruɓanya adadin ƙuri’un da za ta buga. Wato idan masu zaɓe su miliyan 93, to INEC kan buga miliyan 186, ko da za a kai ga yin zagaye na biyu na zaɓen.
“Ana bugo ƙuri’un a lokaci ɗaya, saboda dokar ƙasa ta ce a yi zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa, idan a zagaye a farko aka kasa samun wanda ya yi nasara,” inji Okoye.
“Dalilin bugo su a lokaci ɗaya kuwa, saboda dokar ƙasa ta bayar da ratar kwanaki 21 kacal tsakanin ranar da aka yi zaɓen farko da kuma ranar da za a yi zagaye na biyu.”
Waɗanda Za Su Yi Zagaye Na Biyu:
INEC na shirya zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu ne, “idan aka kasa samun wanda ya yi nasara a zagaye na farko.
“Dokar ƙasa ta ce tilas wanda zai yi nasara ya fi sauran ‘yan takara yawan ƙuri’u. Kuma tilas ya samu aƙalla kashi 1/4 na kashi 2 bisa bisa 3 na ƙuri’un da aka kaɗa a jihohi da FCT Abuja.
“‘Yan takara biyu ne za su iya shiga zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa, daga cikin jam’iyyu 18 da su ka shiga takara.
“Na farko shi ne wanda ya fi kowa yawan ƙuri’u, amma ya kasa samun aƙalla kashi 1/4 daga kashi 2 bisa 3 na yawan ƙuri’un jihohi da FCT Abuja.
“Sai kuma na biyun wanda zai yi zagaye na biyun ɗin, shi ne ya zo na biyu wajen samun kashi 1/4 na kashi 3 bisa 4 na ƙuri’un da aka kaɗa a jihohi da FCT Abuja.”
Okoye ya ƙara da kawo sashe na 134, ƙaramin sashe na 1 na Dokar Gwamnatin Tarayya, wanda ya wajibta sai wanda ya fi saura fifikon ƙuri’u ne za a ayyana cewa shi ya yi nasara.
Ya shaida cewa dukkan ƙuri’un da za a kaɗa da sauran kayan zaɓe su na ajiye a Babban Bankin Najeriya (CBN).
“Na’urar tantance adadin ƙuri’un da aka kaɗa da tantance masu zaɓe, wato BVAS ne kaɗai ba mu bai wa CBN ajiya ba. Wannan kuwa saboda su na da matuƙar muhimmancin da su na wajen mu, bisa tsauraran matakan kulawar ɓangarorin jami’an tsaro,” inji Okoye.