Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin murkushe Boko Haram gaba daya idan har aka zabe shi ya jagoranci Nijeriya a 2023.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya bayyana hakan ne a Jihar Gombe a wajen taron yakin neman zaben jam’iyyar PDP.
- 2023: Idan Ka Isa Ka Shirya Tattaki Irin Namu A Kano – Ganduje Ya Kalubalanci Kwankwaso
- Girgizar Kasa Ta Kashe Mutum 56 Ta Jikkata Daruruwa A Indonesia
“Zan kawar da Boko Haram. Boko Haram ba komai ba ce. Mun kawar da Boko Haram a Adamawa.
“Me zai hana mu yin haka a Borno ko Yobe ko kuma a duk inda suke a kasar nan?” a cewarsa.
Atiku ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta gina hanyoyin da za su hade yankin Arewa maso Gabas.
Atiku, wanda ya ce ba za a iya cika alkawuran da ya dauka ba idan ba zaman lafiya ba, ya ce gwamnatin PDP za ta samar da dukiya da ayyukan yi.
Dan takarar ya yi nuni da cewa zai ga cewa wutar lantarki da za a samar daga Dam din Dakin-Kowa don ciyar da yankin Arewa maso Gabas gaba daya.
Atiku ya shaida wa magoya bayansa cewa gwamnatinsa za ta bunkasa harkar noma domin tabbatar da cewa wadanda ke bangaren sun samu damar yin aiki a lokacin damina da rani.