Kasar Argentina ta kwashi kashinta a hannun Saudiyya a wasan farko na rukunin ‘C’na gasar cin kofin duniya da ake yi a Kasar Qatar.
Dan wasan Argentina Lionel Messi ne ya fara saka kwallo a ragar Saudiyya a minti na 10 daga bugun kai sai mai tsaron raga.
- Sin Ta Samar Da Yanayi Maras Gurbata Muhalli A Gasar Cin Kofin Duniya Na Qatar
- An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe
Bayan dawowa daga hutu ne Saudiyya ta tashi haikan, inda dan wasanta Saleh Al-Shehri ya warware kwallon.
A minti na 53 ne dan wasan gaban Saudiyya Salem Al-Dawsari ya kara kwallo ta biyu.
Haka dai aka tashi wasan, wanda Argentina ta gaza kai bantenta wajen caskala Saudiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp