A yau Laraba 23 ga watan Nuwamba, 2022 ne kotun daukaka kara da ke Sokoto za ta yanke hukunci kan karar da Injiniya Ibrahim Shehu Bakuoye Gusau da Hafiz Nahuche suka shigar a kan Dokta Dauda Lawal Dare da jam’iyyar PDP.
Idan dai ba a manta ba a ranar Juma’ar da ta gabata ne lauyoyin Gusau suka shigar da karar farko na kin amincewa da karar da Lawal ya shigar yayin da babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau a Jihar Zamfara ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar a Zamfara.
- Sin Da Afirka Na Yin Tasiri Mai Yakini A Duniya
- Xi Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Ilimi Karo Na 16 Na Cibiyoyin Kimiya Na Kasashe Masu Tasowa
Mai shigar da karar ya kuma yi gardama kan jam’iyyar PDP, Adamu Maina Waziri da kuma dan takarar kujerar Sanata a Zamfara ta Arewa, Kanar Bala Mande, inda suke kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara.
Kotun ta tanadi hukuncin ne bayan kammala shari’ar a ranar Juma’a kuma ta yi alkawarin sanar da bangarorin ranar da za su yanke hukunci kan bukatar.
Dare da wasu mutane uku suna rokon kotun daukaka kara da ke Sokoto ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Gusau ta yanke wanda ya soke zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayun 2022.
Sai dai Injiniya Ibrahim Shehu da Alhaji Hafiz Nahuche suna kalubalantar hurumin kotun daukaka kara da ta yi watsi da karar a bisa hujjar cewa bangarorin biyu sun yanke hukunci daya; don haka su gudanar da sabon zaben fidda gwani kamar yadda babbar kotun tarayya da ke Gusau ta bayar.