Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da sabbin takardun kudin Naira a fadar shugaban kasa.
Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudin ne a safiyar ranar Laraba a gaban kwamitin majalisar zartarwa na tarayya a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
- Bayan Sauke Darakatan NYSC, Christy Za Ta Rike Mukamin Na Wucin Gadi
- Masari Ya Barke Da Kuka Yayin Gabatar Da Kasafin Kudinsa Na Karshe
Daga cikin sabbin takardun kudin Naira da aka kaddamar akwai N200, 500, da kuma N1000 wanda su ne tun asali aka shirya sauya wa fasali.
Godwin Emefiele, gwamnan Babban Bankin Nijeriya (BN), ya halarci bikin kaddamar da takardun Naira.
A ranar Talata ne, Gwamnan CBN ya shaida wa manema labarai cewa, za a fitar da sabbin takardun ne domin amfanin jama’a.
Ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen taron kwamitin kula da harkokin kudi na CBN (MPC).
Har ila yau, Emefiele ya ce ba za a sauya wa’adin mayar da tsofaffin takardun kudi zuwa ga bankunan kasuwanci ba domin musanya su da sabbi.
Tuni dai wasu ke nan wannan sauyi na takardun kudi bai zo a lokacin da ya dace, amma gwamnatin tarayya ta ce ta shirya komai a kan lokacin da ya dace.