A farkon makon nan, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya kafa tarihin fara hako danyen mai a Arewacin kasar nan da aka samu a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe sama da shekaru 63 da suka wuce tun bayan da aka faro hako irinsa na farko a Oloibiri da ke jihar Bayelsa.
An fara hako danyen Mai da Iskar Gas din a hukumance ne daga kogin Kolmani a karkashin gagarumar kwangilar da aka yi wa lakabi da ‘Kolmani Integrated Debelopment Project’ (KIPRO) da ke kauyen Barambu a Alkaleri da ke Jihar Bauchi.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5, Sun Kama Wani Guda Daya
- Zan Magance Rashin Aikin Yin Matasa Da Dala Biliyan 10 – Atiku
Rijiyar da aka samu man ta Kolmani II na tsakanin jihohin Bauchi da Gombe mai lasisin binciken mai na 809 da 810 da ya hada da wasu karin koguna guda shida da suka kunshi kogin Gongola da ke Tafkin Benuwai.
Ana sa ran Nijeriya za ta samu gangar Mai biliyan daya a karin farko daga kogin na Kolmani sannan idan bincike ya yi nisa kuma za a iya samun ganga biliyan 19, kamar yadda masana suka shaida.
Kazalika, ana sa rai a kullu yaumin a rika hako gangar mai sama da dubu 50 a kullu yaumin somin tabi, sannan akwai matatar mai da za a kafa wadde za ta rika samar da sama da sundukan gas miliyan 500 a kullum, da tashar wuta mai samar da karfin lantarki megawat 300 da kuma Kamfanin takin zamani da zai rika samar da tan 2,500 a kullum.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar kogin Kolmani zai janyo masu zuba hannun jari a bangaren albartaun Mai wanda hakan zai taimaka wa kasar nan sosai wajen kyautata tattalin arziki da shawo kan matsalolin talauci da fatara a cikin kasar nan.
Kan hakan, shugaba kasa Muhammadu ya umarci kamfanin mai na kasa NNPP, da ya zurfafa amfani da kwarewa da kayan aikinsa wajen jawo hankalin masu zuba hannun jari, ya kuma umarce su da su kara himma wajen binciko wasu karin albartun Mai a yankin Arewa da kudu kamar Anambara, Sokoto, Benuwai da kuma Jihar Neja domin wadata kasar nan da arziki.
Buhari ya misalta fara hako Man a matsayin wani babban tarihi ga tattalin arzikin kasar nan, yana tabbatar da cewa ganowa da samo danyen mai a Arewa wani mataki ne da zai kara bai wa Nijeriya kwarin gwiwar samun arzikin makamashi, arzikin kudi da kuma tsaro ta fuskadin abinci a Nijeriya.
Ya de, babban abun farin ciki da dadi da wannan nasarar da aka samu, kasar nan za ta kara samun dumbin masu zuba hannun jari daga sassan duniya daban-daban wanda hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, fadadar tattalin arziki, wadatuwar Mai da Iskar gas da kuma ci gaba mai ma’ana.
Shugaban kasar, ya kuma jinjina wa kamfanin NNPC da sauran masu ruwa da tsaki bisa wannan nasarar da aka samu zuwa yanzu a Kogin Kolmani na II a bisa tsayuwar dakarsu da kuma jajircewarsu.
A jawabinsa, karamin ministan albartun Mai, Timipre Sylba, ya de, kai wa ga wannan matakin na fara hako mai a Kolmani wata gagarumin nasara de ga bunkasar tattalin arzikin Nijeriya da kuma albartun Mai.
Har ila yau, shi ma a wajabinsa, babban manajan gudanarwa na kamfanin NNPC, Dakta Mele Kyari, ya tabbatar da cewa, muddin aka ci gaba da fadada bincike tabbas za a kara samun wasu albartun Mai din, “Tabbas muna da kwarin guiwar wannan matakin zai taimaka wa gwamnati mai ci wajen bunkasa tsaro a arewa maso gabas.”
Mele Kyari ya jinjina wa irin gudunmawar da gwamnonin arewa su 19 suka bayar wajen ganowa da hako mai din, inda ya nuna cewa tabbas kasar ce gaba daya ma za ta mori wannan albartun da aka samu.
Da yake nasa jawabin, Gwamnan Jihar Bauchi , Bala Muhammad, ya de, jihohin Bauchi da Gombe suna cike da murna da farin ciki kan wannan nasarar da aka samu na ganowa da fara hako mai a kogin Kolmani II da ke cikin iyakar karamar hukumar Alkaleri, Bauchi da kuma karamar hukumar Akko da ke jihar Gombe, kana ya ce, babu wata rigima ko tashin hankali da ake samu a tsakanin yankunan.
Bala ya ce, “Dukkaninmu kanmu a hade yake a wannan fannin,” ya kuma ce, samuwar mai a yankin dukka zai amfani kowace jiha ta Gombe da Bauchi da ma kasar nan baki daya, don haka abu ne na murna gaba daya.
“A matsayinmu na gwamnati tuni muka maida hankali a wadannan bangaren na samar da yanayin tafiya da kowa da kuma amfani da hikima da basira domin rage kaifin talauci da fatara a tsakanin al’ummominmu.”
Ya ba da tabbadin cewa, jihohin biyu za su di gaba da bai wa gwamnatin tarayya hadin kai da goyon baya domin dimma manufofinta na kare rayuka da dukiyar al’umma hadi da bunkasa tattalin arziki da wadatar da jama’ar kasa.
A gefe guda, gwamna Bala Muhammad ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari dikin gaggawa da ya ba da umarnin fara gina hanyoyi a yankunan domin saukaka zirga-zirga da jigilaa abubuwan da suka kamata.
“Idan aka kammala gina hanyoyin, zai taimaka wajen bai wa masu zuba hannun jari damar zuwa, zai kyautata tsaro da saukaka wa ma’aikata hadi da al’ummomin da suke yankin.”
Daga nan ya bai wa masu sha’awar zuba hannun jari tabbacin cewa akwai Aminci, tsaro, kwanciyar hankali a kauyen Barambu da ke Alkaleri kuma za su samu kyakkyawar hadin kai daga gwamnatin jihar Bauchi da Gombe dukka domin cimma nasarorin da aka sanya a gaba.
Bala Muhammad ya shaida wa shugaban kasar cewa, wannan aikin fara hako mai din na daga dikin muhimman tarihin da gwamnatinsa suka cimma, don haka ne ya de, al’ummomin Bauchi da Gombe za su dauki tsawon shekaru suna murna da farin diki da wannan nasarar da aka samu.
Shi ma da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce fara hako man a yankin wani mafarki ne da suka jima suna yi sai yanzu Allah ya tabbatar musu, don haka ne suka nuna cewa, shugaban kasa Buhari ya kafa wani tarihin da ba za a taba mancewa da shi ba.
Inuwa ya nuna hakan a matsayin wani karin kyautata tattalin arziki da tsaro inda ya jinjina wa shugaban kasa wajen tabbatar da tsaro a shiyyar arewa maso gabas kuma ya kara da cewa wannan kafa tarihin fara hako mai din zai kara ba da dama wajen kyautata harkokin tsaro.
Ya ce, jama’ar jihohinsu a cike suke da murna kuma tabbas za su jima suna wannan farin cikin bisa wannan nasarori da aka cimma. Ya gode wa dukkanin masu ruwa da tsaki da suka taka rawa har aka kawo wannan matakin.
A gefe daya kuma, mazauna kauyen da aka shiga gonakansu sun koka sosai a bisa rashin samun kudaden Diyya na filayensu da gwamnatin ba ta ba su ba, inda suka nemi agajin Gwamnati ta hannun kamfanin NNPC da su yi wa Allah su biya su diyyar domin rage radadi.
Wasu masu filayen da wakilinmu ya zanta da su jim kadan bayan kaddamar da aikin, sun shaida cewar sun so su sama damar da shugaban kasar zai ji korafinsu amma sakamakon hana su ketare layi muryarsu bai kai a ji ba, inda suka nemi ‘yan jarida da su taimaka musu domin a san halin da suke diki.
Daya daga dikin masu filin Haruna Adamu wanda manomi ne kuma mai kiwo a kauyen Barambu, ya de, “Wannan filin da ake aiki yanzu haka a cikin filayenmu ne da muke noma a ciki. An samu albarkatun kasa a wannan wajen, masu wannan aikin sun ki biyanmu din diyya har zuwa yau.
“Sannan ana aikin nan mu jama’ar wannan kauyen an maida mu kamar ba mu da wani amfani, domin ba mu cin gajiyar aikin da ake yi, sai dai wasu su zo su di arziki a wajen, ba su nemanmu a ciki ko da leburanci ne, sun kuma hana mu noma a filin,” In ji shi.
Haruna Adamu ya shaida cewar ya share sama da shekara talatin yana noma a wannan filin, “Ba za mu zauna babu abincin ba ai, yanzu na samu dan wani karamin fili ina noma a kauyen Fandako amma kuma abinci ba ya isata. Haka da sauran daruruwan wadanda wannan abun ya shafa.”
Ya bayyana cewar duk da suna murna da wannan abin di gaban da kasa ta samu na Mai a wannan yankin, amma ya dade a kale su da idon rahama, “muna murna sosai da wannan ci gabar, amma kuma muna kuka sosai. Don haka muna kira ga gwamnati da ta shigo cikin lamarin, domin tausaya mana.”
Taron bikin kaddamar da fara hako Man, ya samu halartar kusan dukkanin gwamnonin Arewacin Nijeriya da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; da babban manajan gudanarwa na NNDD, Shehu Usman Mai-Borno da kuma Manajan gudanarwa na kamfanin SEEPDO Limited, Mr. Mohit Barot, hadi da sauran masu ruwa da tsaki.
Sai dai kuma wasu na kallon cewa a daidai lokadin da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da wani rahoton da ke cewa jihohin arewa na fama da mafi muni na farata a daidai wannan lokaci, ana kallon fara hako danyen man zai iya nasara wajen rage kaifin fatara da talaudi a tsakanin al’ummomin yanki na arewa.