Wani bincike da jaridar Newyork Times ta gudanar ya nuna cewa gida mafi tsada a Duniya Mallakin Yarima Muham-mad Bin Salman ne wanda aka saya a kan Dala miliyan dari uku ($300m).
Gidan French chateau an yi gwanjon sa ne a 2015 amma daga bisani jaridar ta gano cewa yarima Muhammad ne ya saye gidan.
- Kotu Ta Sutale Tonye Cole A Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC A Ribas
- An Bude Bikin Anime Na Kasa Da Kasa Karo Na 18 A Hangzhou
An boye wa Duniya sanin ko waye ya saye gidan, amma kuma binciken da jaridar ta yi ya bankado yadda aka yi am-fani da wasu Kamfanoni wanda Yariman ke shugabanta a France da Ludembourg aka sayi gidan.
Tun ba yau ba dai aka sha zargin ‘yan gidan sarautar Sau-ciya da yin rayuwa irin ta almubazzaranci da dukiyar jama’ar kasar ta Sauciya wanda gidan sarautar Sauciyar ta sha musantawa.
Jaridar New York Times ta Amurka, ta rawaito cewa Yariman na Sauciyya, Mohammed Bin Salman, shi ne ya sayi wani gida na alfarma a boye a kasar Faransa.
Jaridar ta ce, takardun cinikin gidan da aka yi a shekarar 2015, an gano cewa shi ya sayi gidan ta hanyar amfani da wasu dumbin kamfanoni da aka yi wa rijista.
Gidan wanda ke dab da fadar shugaban kasar Faransa, yana da wurin ajiyar giya na karkashin kasa da sinima da korama da kifaye masu alfarma nau’in koi, da sturgeon da kuma wurin shakatawa na alfarma da ke karkashin kasa.
Kucin gidan dai ya kai dala miliyan 320, wanda mujallar For-tune ta kira shi da gidan da ya fi sauran gidaje tsada a duni-ya.
Mai magana da yawun ofishin jakadancin Sauciyya a Amurka, ta zargi ma’aikatan jaridar da yin rahoto son rai.
Yarima Muhammad bin Salman na Saucia sarkin kasar a yanzu, na yaki da cin hanci da rashawa a kasar
A watannin baya-bayan nan, Yarima Mohammed, ya jago-ranci yaki da cin hanci da rashawa da cin amanar kasa da kuma yadda ake nuna wa wasu gata a kasarsa.
A shekarar 2015, an rawaito cewa, yariman ya sayi wani jirgin ruwa na alfarma daga wajen wani hamshakin dan kasuwa a Rasha a kan kuci dala miliyan 590.
Kazalika jaridar ta New York Times, ta rawaito cewa shi ne kuma ya sayi wani zane na Salbator Munci, wanda Leonar-do da Binci ya yi a kan kuci dala miliyan 450. Daga BBC