• English
  • Business News
Tuesday, August 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wata Mata Ta Shiga Hannu Kan Zargin Kashe Kishiyarta Da Tabarya A Bauchi

by Sadiq
3 years ago
in Manyan Labarai
0
Wata Mata Ta Shiga Hannu Kan Zargin Kashe Kishiyarta Da Tabarya A Bauchi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Rundunar ‘yansanda Jihar Bauchi, ta cafke wata mata mai suna Maryam Ibrahim ‘yar shekara 20 bisa zargin kashe uwargidanta, Hafsat Ibrahim da tabarya.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammad Wakil, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a yammacin ranar Litinin, ya ce an kama wanda ake zargin Maryam Ibrahim da ke kauyen Gar, Pali a karamar hukumar Alkaleri a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022.

  • Jigon PDP Haladu Mohammed Ya Sauya Sheka Zuwa APC A Yobe
  • Matasan Sin Masu Fasaha Sun Lashe Lambobin Yabo Bakwai A Gasar Duniya

A cewar kakakin, mijin matar mai shekaru 40 mai suna Ibrahim Sambo da ke kauyen Gar da ke karamar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi a ranar 22 ga Nuwamba, 2022, ya kai rahoton faruwar lamarin a hedikwatar ‘yansanda ta Maina-maji.

SP Wakil ya ci gaba da cewa, Ibrahim Sambo ya ruwaito cewa “a wannan rana da misalin karfe 12:00 na dare, matarsa ​​ta biyu Maryam Ibrahim mai shekaru 20 da haihuwa a adireshin ta yi amfani da wata tabarya ta buga wa matarsa ​​ta farko Hafsat Ibrahim a kanta.

Leadership Hausa ta tattaro cewa mijin marigayiyar ya sanar da ‘yansanda cewa a sakamakon haka, wadda aka kashe ta samu munanan raunuka kuma an kai ta cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke kauyen Gar inda wani likita ya tabbatar da mutuwarta.

Labarai Masu Nasaba

Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi

Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna

“Lokacin da aka samu rahoton, wata tawagar jami’an tsaro da ke aiki a rundunar ta dauki matakin kama wadda ake zargin”, in ji kakakin.

Ya kara da cewa a lokacin da ake mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amince da aikata laifin da ake zarginta da shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'YansandaBauchiKisaKishiyaMataUwar Gida
ShareTweetSendShare
Previous Post

Jigon PDP Haladu Mohammed Ya Sauya Sheka Zuwa APC A Yobe

Next Post

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Hutun Mako 2 Ga Ma’aikata Maza Da Matansu Suka Haihu

Related

Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
Manyan Labarai

Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi

6 hours ago
Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna
Manyan Labarai

Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna

7 hours ago
Jiragen Saman NAF Sun Kai Hari Kan Taron ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara
Manyan Labarai

Jiragen Saman NAF Sun Kai Hari Kan Taron ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara

14 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15

20 hours ago
Ƴansanda Sun Kama Makashin Wani Ɗan Jarida A Abuja Bayan Shekara Ɗaya
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Kama Makashin Wani Ɗan Jarida A Abuja Bayan Shekara Ɗaya

1 day ago
Yadda Wasu Jihohi Suka Yi Watsi Da Gine-ginensu Da Ke Legas
Manyan Labarai

Yadda Wasu Jihohi Suka Yi Watsi Da Gine-ginensu Da Ke Legas

1 day ago
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Hutun Mako 2 Ga Ma’aikata Maza Da Matansu Suka Haihu

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Hutun Mako 2 Ga Ma'aikata Maza Da Matansu Suka Haihu

LABARAI MASU NASABA

Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi

Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi

August 11, 2025
Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna

Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna

August 11, 2025
An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK

An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK

August 11, 2025
Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli

Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli

August 11, 2025
Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Don Yi Wa Iyalan Ogbeh Ta’aziyya

Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Don Yi Wa Iyalan Ogbeh Ta’aziyya

August 11, 2025
Manoma 2 Sun Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Rikicin Filin Gona A Yobe

Manoma 2 Sun Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Rikicin Filin Gona A Yobe

August 11, 2025
Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 

Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 

August 11, 2025
Sin Ta Kammala Yi Wa Yankuna 5 Na Kare Muhalli Da Halittu Na Kasar Rajista

Sin Ta Kammala Yi Wa Yankuna 5 Na Kare Muhalli Da Halittu Na Kasar Rajista

August 11, 2025
Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC

Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC

August 11, 2025
Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro

August 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.