Gamayyar matan Kiristocin Arewa 414 a karkashin kungiyarsu ta (NCWC), sun yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar mubayi’a domin tabbatar da ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Gamayyar matan, sun fito ne daga jihohin kasar nan 19 ciki har da Abuja, sun ayyana goyon bayansu ga Atiku ne a taron da suka gudanar a dakin taro da ke a cibiyar mata da ke Abuja, inda suka shelanta cewa, za su shiga har zuwa cikin kauyukan kasar nan domin samar wa da Atiku dimbin kuri’u.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Hutun Mako 2 Ga Ma’aikata Maza Da Matansu Suka Haihu
- Jigon PDP Haladu Mohammed Ya Sauya Sheka Zuwa APC A Yobe
Sun kuma bayyana Atiku a matsayin mutumin da ba ya nuna kabilanci, inda suka yi nuni da cewa, Nijeriya za ta kasance ne kawai a cikin wadataccen tsaro idan aka zabi Atiku a matsayin shugaban kasar nan.
A Jawabinta, shugabar kungiyar ta (NCWC) Princess Leah Solomon, ta ce, ya kamata ‘yan Nijeriya su yi farin ciki da samun Atiku, inda ta kara da cewa, matan kiristocin za su tabbatar da cewa, Atiku ya lashe zaben 2023.
Leah, ta ce burinta shi ne ganin an hada kan ‘yan Nijeriya a waje daya, inda ta ce, mutane da dama ba sa jin dadin samun rabuwar kawunan ‘yan kasar nan, saboda yunwa yara ba sa iya zuwa makarantunsu don neman ilimi.
Ta ce, kimanin kungiyoyin mata kiristanci 414 ne da suka fito daga Arewa suka halarci taron kungiyar, inda ta ce “Muna son Atiku kuma shi za mu yi wa aiki, domin yana da dukkan kwarewar da ake bukata ta zama shugaban kasar nan.”