ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NIS Ta Ƙaddamar Da Sabon Ingantaccen Fasfo A Ƙasar Kanada

CGI Isah Jere Ya Ce Za A Kawar Da Tsaikon Da Ake Samu Wajen Samun Fasfo

by yahuzajere
3 years ago
fasfo

Kwanturola Janar na NIS, CGI Isah Jere Idris (a dama) yayin da yake taya Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola kaddamar da sabuwar cibiyar bayar da ingantaccen fasfo a ofishin jakadancin Nijeriya da ke Ottawa, kasar Kanada

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta ƙaddamar da sabon ingantaccen fasfo da ake wa laƙabi da “enhanced e-passport” tare da buɗe ofishin da zai riƙa samarwa a Ottawa da ke yankin Ontario a ƙasar Kanada, domin bai wa ‘Yan Nijeriya mazauna ƙasar damar samun sabon fasfon mai matakai daban-daban.

Nijeriya dai tana daga cikin ƙasashe biyar na duniya kuma ta farko a Afirka da suka samar da sabon ingantaccen fasfon. Shi dai sabon fasfon, an tsara shi ne da fasahohin zamani tare da inganta tsaro a cikinsa da kuma ƙara yawan samfuransa ciki har da mai shafi 64 da ke aiki har na tsawon shekara 10 domin ƙara kyautata walwalar ‘Yan Nijeriya masu balaguro a ƙasashen duniya.

  • Kayan Angonci Sun Yi Batan Dabo, An Sace Sadakin Amarya A Taron Daurin Aure A Kano

Sakamakon tsaron da aka ƙara a sabon fasfon ta fuskoki 25 fiye da wanda ake amfani da shi a yanzu, maɓarnata da masu satar shaida ba za su iya amfani da shi ba wajen damfara.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi a yayin ƙaddamarwar, Kwanturola Janar na NIS, CGI Isah Jere Idris, ya bayyana cewa duk da fara bayar da sabon ingantaccen fasfon a Kanada, za a ci gaba da bayar da tsohon da sabon a tare har zuwa lokacin da za a kammala aikin fasfunan da aka nema a baya.

“Za a ci gaba da bayar da sabon ingantaccen fasfon da kuma wanda ake bayarwa kafin zuwan sabon har sai lokacin da aka mayar da ɗaukacin cibiyoyin bayar da fasfo zuwa na sabon da aka samar”, ya bayyana.

LABARAI MASU NASABA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Fasfo
CGI Isah Jere (na biyu a dama) yayin da Ministan Cikin Gida Aregbesola yake miqa wa Jakadan Nijeriya a Kanada, Mista Asekun sabon ingantaccen fasfon da aka kaddamar

Har ila yau, CGI Isah Jere ya ce za a magance tsaikon da ake samu wajen yi wa mutane fasfo matuƙar masu nema suna bin matakai da ƙa’idojin da aka shimfiɗa ta hanyar tabbatar da cewa sun gabatar da buƙatarsu ta fasfo ta shafin intanet tare da biyan kuɗi ta nan, da daidaita bayanan fasfonsu su yi daidai da bayanan da ke ƙunshe a katinsu na shaidar ɗan ƙasa (NIN).

Isah Jere ya ƙara jaddada cewa NIS za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta sauke nauyin da tsarin mulkin ƙasa ya ɗora mata tare da kyautata mu’amala da abokan hulɗa a ko ina cikin faɗin duniya.

A nashi jawabin tun da farko, Ministan Cikin Gida, Rauf Ogbeni Aregbesola, ya bayyana cewa sakamakon ƙaddamar da ofishin sabon fasfon a Kanada, a halin yanzu ‘Yan Nijeriya mazauna can za su iya shiga shafin NIS na intanet su gabatar da buƙatunsu na fasfo kai-tsaye.

  • Daga Yanzu Wajibi Ne A Koyar Da Yara Da Harshen Gado A Firamare – Gwamnati

Ya ce, wa’adin da aka ɗiba ga mai neman sabon fasfo shi ne za a yi masa a cikin mako shida, yayin da wanda zai sabunta kuma za a yi masa a cikin mako uku. Waɗannan makonnin da aka ɗiba a cewar ministan, domin a bai wa NIS sarari ne ta yi bincike game da bayanan da mai neman fasfo ya gabatar da kuma tabbatar da ingancin aikin kamar yadda ake yi a duk ƙasashen duniya da suka ci gaba.

fasfo
Kwanturola Janar na NIS, CGI Isah Jere Idris (a hagu), Jakadan Nijeriya a Kanada, Mista Adeyinka Asekun da Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola yayin kaddamarwar

Haka nan ya nanata muhimmancin daidaita bayanan fasfo da na katin ɗan ƙasa (NIN), domin a cewarsa, ana matuƙar samun matsala kan haka kuma da zarar an samu bambanci komai ƙanƙanta, za a samu tsaiko wajen aikin fasfon.

Wakazalika, da yake tofa albarkacin bakinsa, Jakadan Nijeriya a Kanada, Mista Adeyinka Asekun ya yaba wa Ministan da Kwanturola Janar na NIS bisa hoɓɓasar da suka yi wajen ƙaddamar da sabin ingantaccen fasfon a Kanada wanda ya ce ita ce ta uku da NIS ta samar da sabon fasfon baya ga Amurka da Ingila.

Ya shawarci ‘Yan Nijeriya da ke ƙasar su yi ƙoƙari su ci gajiyar wannan damar da NIS ta samar musu musamman wajen neman fasfo mai shafi 64 da ke aiki na tsawon shekara 10 wanda ake iya neman sabuntawa tun ana saura shekara ɗaya wa’adin aikinsa ya ƙare.

 

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Next Post
Kotu Ta Bayar Da Umarnin A Cafko Mata Shugaban Sojojin Nijeriya, Faruk Yahaya

Kotu Ta Bayar Da Umarnin A Cafko Mata Shugaban Sojojin Nijeriya, Faruk Yahaya

LABARAI MASU NASABA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.