Shugaba Muhammadu Buhari, ya soki gwamnonin kasar nan bisa karkatar da kudaden da ake tura wa kananan hukumomi da ke a daukacin fadin kasar.
Buhari ya yi wannan sukar ne a jawabinsa a gurin taron kwas na manyan jami’an cibiyar NIPSS karo na 44 na shekarar 2022, da ya gudana a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Da Dumi-Duminsa: Kotu Ta Tabbatar Da Adebutu A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Ogun
- An Garkame Dalibin Da Ya Soki Aisha Buhari A Gidan Yari
Shugaban wanda ya sanar da hakan a yau Alhamis, ya bayyana cewa, kowa zai yi makakin yadda gwamnonin ke karbar kudade kananan hukumomin da ke a jihohinsu da sunansu, amma a karshe gwamnonin sai su rike su.
Ya kara da cewa, irin wannan halin na gwamnonin ke kara haifar da cin hanci da rashawa a kasar nan.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wannan furucin na Buhari kan gwamonin, na zuwa ne bayan awa 24 da majalisar zartarwa ta kasa ta dora alhakkin karuwar talauci a kasar nan, musamman saboda gazawar gwamnonin wajen na bayar da ta su gudunmawar ta samar da ci gaba.
Karamin ministan kudi da tsare-tsaren kasa, Clement Agba, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a jiya Laraba, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, hukumar kididdigar ta kasa NBS, a kwanan baya ta sanar da cewa, ‘yan Nijeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci.
Agba ya sanar da hakan a martanin da ya mayar na tambayar da manema labarai suka yi masa na cewa, shi da ministar kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed wane kokari suke yi don a rage wa akasarin ‘yan Nijeriya radadin talaucin da suke fuskanta a yanzu.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta hanyar shirinta na samar da saukin rayuwa ga ‘yan Nijeriya, na ci gaba da zuba kudade domin a rage wa ‘yan Nijeriya halin kuncin ruwa da suke fuskanta, inda ya bayyana cewa, kashi 72 na talaucin da ake fuskanta, ana samun hakan ne a kananan hukumomi, saboda gwamnonin su, sun yi watsi da al’ummar da ke karkara.
Agba ya kara da cewa, akasarin gwamonin, sun karkatar da yin ayyukansu ne a birane, musamman wajen gina manyan gadoji, gyaran filin jirgin sama da kuma gudanar da wasu manyan ayyuka, maimakon mayar da hankulinsu wajen raya karkara da jama’a.
Ya shawarci gwamnonin da su mayar da hankulinsu wajen samar da shirye-shiyen da za su inganta rayuwar akasarin ‘yan Nijeriya, domin a tsamo su daga cikin radadin talaucin da suke fuskanta.