Kamar yadda aka sani aure wani nau’i ne na ibada wanda yake haifar da nishadi natsuwa da jin dadi. Idan aka ce aure ana nufin sadaukarwa da kuma girmama juna.
Zamantakewar aure abu ne da aka gina shi a kan abubuwa biyu zuwa uku na farko akwai kishin juna na biyu akwai yarda da amana.
- Jerin Kayayyakin Da INEC Ta Yi Asara Bayan Kai Mata Hare-hare A Ofisoshinta
- LP, Ta Kori Daraktan Yakin Neman Zaben Obi, Okupe Da Wasu 11 Kan Gaza Biyan Harajin Jam’iyyar
Idan muka dauki yarda da amana zamu ga cewa wani abu ne da ma’auratan biyu suka damkawa junansu inda zamu ga cewa miji yana kokarin kare duk wani martaba na matarsa haka itama matar.
Idan muka yi dubi da shimfidan da na fara zamu ga cewa an gina zaman aure a kan turaban sadaukarwa da amana, idan kuwa haka ne to me yasa Miji ke juya wa uwargida baya a lokacin da yake kokarin karo aure?
Yawanci maza in sun yi shirin karin aure gaskiya akwai halayya iri daban-daban da uwargida ke cin karo da su a wurin Maigida ,wanda zamu ga cewa gaba daya miji yakan manta irin zaman dadi da kuma zaman hakuri da ta yi da shi.
Hakazalika miji yana sauyawa ta halayya daban-daban ga uwargida inda har wani lokaci in ba a kai zuciya nesa ba saki ko sabani mai karfi na iya shiga tsakani.
Yawanci maza in sun zo karin aure sukan sauya fuska da walwala wa uwargida wanda hakan an yi ittifakin cewa yawanci maza suna ganin cewa si yanzu ita uwargida ta ragwaba bata da sauran mamora shiyasa idon su sai ya kyalla ya fara hango musu wata a waje,wanda har zai kai ga ana diban lokacin uwargida ana baiwa amarya tun kafin ta shigo gidan.
Wani lokaci zakaga idan miji ya fara shirin karin aure zai dauko wasu sababbin halayya wanda uwargida bata sansu ba ya dorawa kansa, kamar misali akwai mijin da zakaga idan yaso karin aure to fa uwargida ta shiga uku don komai ta yi ba ta burge shi ba saima hantara da fada da zai dinga yawan yi mata, ko kuma kaga wani mijin in yaso karin aure to ya daina shiga harkan uwargida musamman da muke da kafafen soshiyal media daban-daban to gaba daya lokacin shi ya zama na amarya ko yaushe suna manne a waya ko kuma suna ‘Charting’ ita uwargida an ajiyeta a gefe an gama yayin ta.
Wani namijin in yaso aure kuma yarasa wani laifi zai mannawa uwargida in aka dameshi da tamabaya wani sai yace ai bata iya tarban baki ba ne saboda a tunanin sa yana ganin kamar ita wacce yake kokarin aurowar tafi kowa hankali ta iya komai dari bisa dari bai san cewa hangen dala yake yi ba.
Wani namijin kuwa sababbin halayensa basa chanzawa sai ya auro ta ya kawo cikin gida daga nan ne labari zai chanza salo in ya hadu da itama amaryar ‘yar garice sai su hada kai da mijin su muzgunawa uwargida, misali akwai gidan da za kaga daga ranar da amarya ta zo to fa baban maganar wanda miji zai saurara akwai gidan da naga amarya ta yi wa uwargida sharrin cewa tana bin malamai saboda tana gane ganecin tana bacci irin wannan sharrin kamata ya yi ace mijin ya yi hukunci mai karfi amma abin mamaki sai ya goyi bayan amarya a kan cewa ya yarda uwargida na bin boka.
Mai yasa, duk tsawon shekarun da suka yi da uwargidan bai fada mata tana bin malamai ba saida ya karo aure, abubuwa makamantan haka suna faruwa a gidajen aure daban daban a duk sanda miji ya dau kdamaran karo aure.