ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tambuwal Ya Gabatar Da Kasafin Kudinsa Na Karshe a Sakkwato

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
3 years ago
Tambuwal

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya gabatar da Naira biliyan 198, 501, 095, 129. 88 a matsayin kasafin kudin shekarar 2023 a gaban Majalisar Dokokin Jihar.

Kasafin wanda shi ne na karshe da Gwamna Tambuwal ya gabatar a mulkinsa na shekaru takwas a wa’adin zango biyu da ya jagoranta, ya karu da kashi 26.7%, wato Naira biliyan 10 a kan na 2022 wanda ya gabatar a kan Naira biliyan 188, 429, 495, 847. 63.

  • Iran Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Wasu Mutane Da Aka Samu Da Laifin Yi Wa Isra’ila Aiki 
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yansanda 3 Da Wasu A Sakkwato 

Kudaden albashi da tafiyar da al’amurran yau da kullum sun samu naira bilyan 41 338, 449, 185. 12 da 42 756 507 973. 65, sai kuma manyan ayyuka da suka samu naira biliyan 111, 406, 137, 971. 11.

ADVERTISEMENT

Kamar a kowane kasafi, fannin ilimi ya samu kaso mafi yawa na biliyan 36, 991, 319, 548. 53 wato kashi 18.6% sai fannin lafiya da ya zo na biyu da naira biliyan 25, 208, 374, 170. 49, sai fannin aikin gona da ya samu naira biliyan 11, 010, 553, 897. 62 (5.5%) a yayin da samar da ruwan sha ya samu naira biliyan 4, 317 715 705. 45 (2.2%)
Sauran fannoni sun samu naira biliyan 116, 917, 145, 031. 49 wato kashi 58.9%.

Manyan ayyuka sun samu kashi 58. 9% na bakidaya kasafin a yayin da al’amurran yau da kullum suka samu kashi 41. 1%. Tambuwal ya ce Kasafin Kudin zai ba da damar kammala dimbin ayyukan da aka assasa da muhimman ayyukan da za a rika tunawa wadanda Gwamnatinsa ta aiwatar.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa

Gwamnan ya godewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, sarakunan gargajiya, malaman Addini da jimlatan din al’ummar Jihar Sakkwato kan goyon bayan da suka baiwa Gwamnatinsa.

Tambuwal ya kuma bukaci hadin kan manbobin Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato domin tabbatar da kudurorin Gwamnatinsa ta hanyar aiwatar da ayyukan raya Jiha da ci-gaban al’umma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman
Kananan Labarai

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

September 26, 2025
Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa
Kananan Labarai

Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa

May 23, 2025
Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya
Kananan Labarai

Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya

April 18, 2025
Next Post
katin zabe

2023: 12 Ga Disamba Za A Fara Raba Sabon Katin Zabe Tsawon Kwanaki 40 - INEC

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.