A karo na uku, an debo samfuran abubuwan binciken kimiyya daga tashar sararin samaniya ta Tiangong mallakin kasar Sin, inda a wannan karo ‘yan sama jannatin kasar na kumbon Shenzhou-14, suka iso da samfuran birnin Beijing a jiya Litinin.
Abubuwan da ‘yan sama jannatin suka iso da su doron duniya, sun hada da tsirran shinkafa 3, da tsiron itacen Arabidopsis, da wata jaka mai kunshe da akwatuna 4 na wasu sinadarai. Tuni aka mika samfuran ga cibiyar binciken ayyukan fasahohin injiniya masu nasaba da samaniya, wadda ke karkashin cibiyar masana kimiyya ta kasar Sin.
Rahotanni sun ce nau’o’in tsirran 2 da ‘yan sama jannatin suka tawo da su daga samaniya, sun shafe kwanaki 120 ana renon su a tashar Tiangong. Ana sa ran masana kimiyya za su nazarce su, domin gano tasirin maganadisun kasa dake sararin samaniya a kan tsirran.
Sashen gudanar da bincike kan sinadarai na dakin gwajin Tianhe, shi ne irin sa na farko da Sin ta kafa a tashar ta Tiangong, shi ne kuma irin sa na biyu a duniya da aka yi amfani da shi a samaniya. Ya zuwa yanzu, dakin binciken ya shafe kwanaki sama da 590 yana aiki yadda ya kamata, ya kuma kammala gwaje-gwaje kan akwatunan sinadarai 7 a tashar ta samaniya. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)