An tsige shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kaduna, Mista Ben Kure daga mukaminsa.
An tsige shi ne a jiya biyo bayan kada kuri’ar rashin amincewa da kwamitin aiki na jam’iyyar NNPP na jihar.
- Dan Haya Ya Maka Mai Gida A Kotu Kan Kin Sayar Masa Da Gidan Da Ya Ke Haya
- Da Dumi-Dumi: Hazard Ya Yi Ritaya Da Buga Wa Belgium Kwallo
Mataimakin shugaban shiyya ta biyu, Hosea Baba ne ya gabatar da kudirin tsige shi, sannan sakataren kungiyar na jiha, Alhaji Sa’ad Idris, Kudan ya goyi bayansa.
Haka kuma an cire tare da shugaban jam’iyyar har da mashawarcin jam’iyyar, Ibrahim Ahmed.
Tuni dai aka maye gurbinsa da tsohon shugaban riko na jam’iyyar NNPP Nuhu Audu.
Audu, wanda ya kasance shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Sanga a jihar ya zama shugaban jam’iyyar na jiha.
Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na jihar, Kanal Albehu Dauda Gora (mai ritaya), ya fitar jim kadan bayan kammala taron ya ce dukkansu Kure da Ahmed sun saba wa tanadin sashe na 31:1 na kundin tsarin jam’iyyar NNPP da sashe na 82 (1) (3) ( 5)&83(1) na Dokar Zabe, 2022 bi da bi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kwamitin ayyuka na jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kaduna, ya gudanar da taro a ranar Talata 06 ga watan Nuwamba, 2022 kuma bayan tattaunawa kan kudirin da mataimakin shugaban shiyyar 2, Hon. Hosea Baba, da sakataren kungiyar na jiha, Alhaji Sa’ad Idris Kudan ya marawa baya, sun kada kuri’ar rashin amincewa da shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kaduna, Ben Kure.